Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 15:17:05    
Beijing ba ta gamu da matsala ba wajen gina filaye da dakunan wasa domin taron wasannin Olympic na shekarar 2008

cri

Yin amfani da wadannan filaye da dakunan wasa bayan taron wasannin Olympic na Beijing shi ma ya yi ta jawo hankalin kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sosai. Don magance daina ci gaba da yin amfani da su da kuma bata albarkatu bayan taron wasannin Olympic na shekarar 2008, wannan kwamiti ya tsara shirye-shirye daban daban domin tabbatar da matukar amfanin wadannan filaye da dakunan wasa. Mr. Wu ya yi karin haske cewa, hukumar Beijing ta raya wadannan filaye da dakunan wasa yadda ya kamata bayan taron wasannin Olympic na Beijing bisa bambancinsu da kuma sigogin musamman masu. Ga misali, filaye da dakunan wasa da aka gina a jami'o'i za su zama cibiyoyin wasannin motsa jiki ga dalibai da matasa. Sa'an nan kuma, 'yan kasuwa za su zuba jari kan wadanda aka gina domin dalilin kasuwanci, za a shirya manyan gasanni da kasaitattun wasannin kida a wadannan filaye da dakunan wasa. Mr. Wu ya ce,'Al al misali, za a yi amfani da dukkanin filaye da dakunan wasa da ke cikin jami'o'i da kuma wadanda aka gina domin dalilin kasuwanci kamar yadda ya kamata. Filaye da dakunan wasa na wucin gadi kuwa, in sun cancanta, to, za a kiyaye wasu daga cikinsu, za a yi namijin kokari wajen zuba jari a kansu domin ci gaba da yin amfani da su.'

To, madalla, masu sauraro, karshen shirinmu na yau na wasannin motsa jiki ke nan, ni Tasallah da na gabatar nake cewa, ku huta lafiya, sai mako na gaba, in Allah ya kai mu.(Tasallah)


1 2 3