Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 15:17:05    
Beijing ba ta gamu da matsala ba wajen gina filaye da dakunan wasa domin taron wasannin Olympic na shekarar 2008

cri

Mr. Wu ya kara da cewa, a cikin filaye da dakunan wasa guda 31 domin taron wasannin Olympic na Beijing, 12 daga cikinsu ne aka soma ajiye injunan wutar lantarki. A cikin filaye da dakunan wasa guda 11 da ake yi musu kwaskwarima, an gama ayyuka a filin wasa na wasan kwallo mai laushi na Fengtai, saura 10 kuwa ana kusan kammala gina su, ana ajiye tsarin bututu a ciki da kuma yi musu ado. Kazalika kuma, an kaddamar da ayyukan filaye da dakunan wasa guda 8 na wucin gadi duka. Dangane da lokacin da za a kammala gina dukkan filaye da dakunan wasa, Mr. Wu ya bayyana cewa, ayyukan yawancin wadannan filaye da dakunan wasa za su kare kafin karshen wannan shekara. Ya ce,'Ban da babban filin wasa na kasar Sin da kauyen kafofin yada labaru da kuma gine-ginen da ke shafar taruruka, za a gama gina sauran filaye da dakunan wasa da gine-ginen da abin ya shafa a karshen wannan shekara daya bayan daya.'

Mr. Wu ya ci gaba da cewa, za a kawo karshen gina filaye da dakunan wasa da gine-ginen da abin ya shafa misalin guda 20 a watan Yuli zuwa na Satumba na shekarar da muke ciki. Za a kuma kammala gina wasu 10 kafin karshen wannan shekara.

Dadin dadawa kuma, a lokacin da ake gina filaye da dakunan wasa, ana bin tunanin 'shirya taron wasannin Olympic ta hanyar kimiyya da fasaha ta zamani, tare kuma da mai da hankali kan al'adu da kiyaye muhalli'. Yanzu ayyukan da ke shafar taron wasannin Olympic sun sami sakamako mai kyau a fannonin tsara tsarin gaba daya da yin tsimin albarkatun ruwa da yin amfani da sabon makamashi da dai makamantansu.


1 2 3