Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-13 15:56:47    
Masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin suke kara samar da guraben aikin yi masu yawa ga mutanen kasar

cri

A sakamakon ci gaba da masana'antu masu zaman kansu ke samu cikin sauri, dalibai da suka gama karatu daga jami'o'in gida da na waje su ma suna sha'awar samun aikin yi a masana'antu masu zaman kansu. Mr Zhu Chenglin, wanda ya sami digiri na farko a jami'ar gida ya bayyana cewa, " a masana'antu masu zaman kansu, ana ciyar da ma'aikata gaba cikin gajeren lokaci ne, kuma ana samar da dama mai yawa wajen ciyar da ma'aikata gaba. Don haka, mai yiwuwa ne, ni ma zan iya samun damar ciyar da ni gaba a cikin irin wadannan masana'antu."

An ruwaito cewa, yawan dalibai wadanda suka gama karatu daga jami'o'i wadanda kuma ba su sami aikin yi ba ya wuce miliyan 1.2 a kasar Sin a shekarar bara. A cikin irin wannan hali ne, masana'antu masu zaman kansu wadanda ke kara samun bunkasuwa za su kara ba da taimakonsu wajen samar da guraben aikin yi ga daliban da ba su sami aikin yi ba. Malam Chu Ping, mataimakin shugaban kungiyar hadin kan masana'antu da kasuwanci ta kasar Sin yana ganin cewa, "bayan da dalibai da suka gama karatu daga jami'o'i da sauran kwararru suka fara samun aikin yi a masana'antu masu zaman kansu, ba ma kawai za a gaggauta bunkasa masana'antun bisa matsayi mai girma ba, har ma masana'antun sun samar da guraben aikin yi ga dalibai da suka gama karatu daga jami'o'i, sa'an nan daliban za su sami dama mai kyau wajen samun ci gaba."

Malam Chu Ping ya kara da cewa, kungiyarsa za ta kara shirya masana'antu masu zaman kansu da yawa da su je jami'o'I don kara daukar dalibai da suka gama karatunsu daga jama'o'in, sa'an nan za ta ba da kwarin guiwa ga daliban da su sami aikin yi a masana'antun nan. (Halilu)


1 2