Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-13 15:56:47    
Masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin suke kara samar da guraben aikin yi masu yawa ga mutanen kasar

cri

Yanzu, masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin suna bunkasuwa cikin sauri sosai, kuma suna kara samar da guraben aikin yi masu yawa ga mutanen kasar. Tun daga shekarar 2001 zuwa ta 2006, matsakaicin yawan guraben aikin yi da suka samar ya kai miliyan 5 zuwa miliyan 6 a ko wace shekara, wato ke nan ya dauki kashi uku cikin hudu na sabbin guraben aikin yi da aka samar a birane da garuruwa na kasar.

Bisa kidayar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar bara, jimlar masana'antu masu zaman kansu ta wuce miliyan 30 a kasar Sin, yawan kudin haraji da suka biya ya wuce kudin Sin Renminbi Yuan biliyan s550. Madam Li Lanyun wadda ke zama a unguwar Heping ta birnin Tianjin da ke a arewacin kasar Sin, an sallame ta daga aiki ne a shekarar 1994, bayan haka ta taba zama mai aikin gida da mai yin shara da goge-goge, daga baya kuma sai ta kafa wani kamfanin yin aikin gida mai zaman kansa. Madam Li Lanyun ita ma ta zama shahararriyar mai masana'antu mai zaman kai a birninta. Ta bayyana cewa, "yanzu, na dauki ma'aikata sama da 600 aiki wadanda aka sallame su daga aiki, ni ma an taba sallamata daga aiki, don haka ya kamata, na dauke su da yawa, don yin aiki tare."

Madam Li Lanyun ta iya samun sakamako mai kyau kamar haka bisa taimakon da ta samu daga manufofin gwamnatin kasar Sin game da ba da kwarin guiwa gare ta. A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, a wurare daban daban na kasar Sin, an dauki matakai da dama wajen rage yawan haraji da ake bugawa a kan masana'antu masu zaman kansu da samar da rancen kudi maras yawa da sauransu, don ba da kwarin guiwa ga 'yan kwadago da su kafa masana'antu masu zaman kansu da samun aikin yi. Ban da wadannan, kasar Sin ta aiwatar da harkoki iri daban daban don taimaka wa masana'antu masu zaman kansu wajen kara samar da guraben aikin yi masu yawa da daukar kwararru aiki.

1 2