Mr. Xu ya ce, ko da yake yanzu yawan matsalolin da suke da nasaba da gonaki yana raguwa, amma har yanzu ba a kayyade yunkurin yin amfani da gonaki ba bisa doka ba kwata kwata. Mr. Xu ya ce, "Haka kuma, mun gano cewa, a cikin asiri ne wasu gwamnatocin birane da na gundumomi suke goyon bayan wasu mutane da su mamaye gonaki ba bisa doka ba, kamar su yin amfani da gonaki kafin samun izini, ko an kafa shiyyoyin raya masana'antu ko kara fadinsu da kansu amma ba tare da neman izini ba. Bugu da kari kuma, ana mamaye gonaki lokacin da ake daidaita babban shirin yin amfani da gonaki. Sannan ana kuma keta moriyar halal ta manoma."
Mr. Xu ya bayyana cewa, ma'aikatar kasa da albarkatu ta kasar Sin za ta ci gaba da duba yadda ake amfani da gonaki domin raya masana'antu domin kara karfin sa ido kan yadda ake amfani da gonaki bisa shari'a. A waje daya, ma'aikatar kasa da albarkatu ta kasar Sin da ma'aikatar sa ido kan ma'aikatan gwamnati na kasar Sin za su dauki matakan musamman domin fama da matsalolin yin amfani da gonaki ba bisa doka ba da kiyaye moriyar hala ta manoman da aka mamaye gonakinsu.
Yanzu kasar Sin tana fuskantar matsaloli biyu masu tsanani, wato tana bukatar isassun gonaki domin tabbatar da samar da isassun hatsin da take bukata, amma a waje daya, ana bukatar kasa da yawa domin raya masana'antu da birane. Game da wadannan matsaloli biyu da ke kasancewa a gaban kasar Sin, Mr. Xu Shaoshi yana ganin cewa, lokacin da ake raya masana'antu da birane cikin sauri yanzu, dole ne kasar Sin ta yi tsimin yankunan kasa. Ya ce, "Yawan gonakin da aka mamaye su amma har yanzu ba a yi amfani da su ba ya kai fiye da kadada dubu 260 tare da yankunan kasa fiye da kadada miliyan 13 da aka yi watsi da su domin dalilai iri daban-dabam kuma da yankunan kasa da yawansu ya kai kadada miliyan 260 da har yanzu ba a yi amfani da su ba. Sabo da haka, muna da yankunan da za mu iya amfani da su domin raya tattalin arzikinsu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne bai kamata a sake ci gaba da yin amfani da gonaki domin raya masana'antu." (Sanusi Chen) 1 2
|