Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-12 18:45:33    
Kasar Sin za ta kara karfi sa ido kan yadda ake amfani da gonaki

cri

Lokacin da kasar Sin take samun bunkasuwar tattalin arziki, yawan gonakin da ake mamaye su yana ta karuwa. Sabo da haka, ya kasance da wasu matsalolin mamaye gonaki ba bisa doka ba. A ran 12 ga wata, Mr. Xu Shaoshi, sabon ministan kasa da albarkatu na kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta kara karfin sa ido kan yadda ake amfani da gonaki da yin bincike kan matsalolin mamaye gonaki ba bisa doka ba domin kiyaye gonaki.

Kasar Sin kasa ce mai dimbin yawan mutane. Matsakaicin gonakin da kowane Basine ke mallaka ya kai kashi 40 cikin kashi dari kawai bisa na matsakaicin gonakin da kowane mutumin duniya ke mallaka. Lokacin da ake samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ana kuma amfani da gonaki da yawa domin raya masana'antu. Yawan gonaki yana ta raguwa a kai a kai a kowace shekara. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da tsarin sa ido kan yadda ake amfani da gonaki mafi tsanani domin rage saurin cigaban tattalin arziki da tabbatar da samun isassun hatsin da ake bukata. Bisa wannan tsari, gwamnatin kasar Sin za ta yi namijin kokari domin tabbatar da gonakin da yawansu ya kai fiye da kadada miliyan 120.

A gun wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya a nan birnin a ran 12 ga wata, Mr. Xu Shaoshi, sabon ministan kasa da albarkatu na kasar Sin ya bayyana cewa, a watan Yuli na shekarar da ta gataba, gwamnatin kasar Sin ta ba da izinin kafa tsarin sa ido kan albarkatun kasa, kuma an kafa hukumomi 9 don sa ido kan albarkatun kasa a duk fadin kasar wadanda suke karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye. Tun daga watan Janairu zuwa watan Mayu na shekarar da muke ciki, yawan haramtattun matsalolin da suke da nasaba da gonaki fiye da kadada dubu 10, kuma aka gano su ya kai fiye da dubu 20. An kuma yi shari'a kan mutane fiye da 100 domin wadannan matsaloli.

1 2