Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-11 08:27:34    
Kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing yana kokarin kyautata aikin hidima ga kafofin watsa labarai

cri

A babban dakin ba da hidima dake bene na biyar na cibiyar watsa labarai na taron wasannin Olimpic na Beijing,gaba daya sassa 29 da abin ya shafa na kasar Sin wadanda suka hada da ma`aikatar harkokin waje da ma`aikatar kiyaye kwanciyar hankali da ma`aikatar sufuri da babbar hukumar kwastan da bankin kasar Sin da kwamitin shirya wasannin Olimpic da dai sauransu sun kafa tasoshin aiki a nan.Manema labaran da zuka zo daga kasashen waje suna iya gama ayyuka iri daban daban cikin sauri.A tarihin taron wasannin Olimpic,ba a taba shirya irin wannan aiki ba a da,shi ya sa ana iya cewa,taron wasannin Olimpic na Beijing ya sabunta aikin ba da hidima na taron wasannin Olimpic.

Kazalika,kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing shi ma ya buga wasu litattafai masu sauki ga manema labarai da suka zo daga kasashen waje da Hongkong da Macao da kuma Taiwan domin ba da hidima ga aikinsu.Mr.Sun Weijia ya yi mana bayani cewa,  `Dalilin da ya sa a buga wadannan litattafai shi ne domin nuna bayani kan ka`idoji da manufofi da abin ya shafa ga manema labarai na kasashen waje da Hongkong da Macao da kuma Taiwan,haka kuma za su gudanar da aiki yadda ya kamata.`

Ban da wannan kuma,kwamitin shirya wasannin Olimpic ya yi kokari domin samar da muhallin aiki mai kyau ga manema labarai,babbar cibiyar watsa labarai ta taron wasannin Olimpic na Beijing za ta fara aiki kafin karshen wannan shekara.Don tabbatar da aikin watsa labarai na taron wasannin Olimpic na shekarar 2008,kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing yana yin iyakacin kokarinsa.Mr.Sun Weijia ya ce:  `Alal misali,muna yin nazari kan wani batu,wato za a kafa wani babban dakin aiki mai dauke da mutane dubu daya a babbar cibiyar watsa labarai,kuma za a ajiye wasu teburorin aiki a ciki,amma game da wurin hada lantarki,muna yin la`akari sosai saboda kayayyakin lantarki na manema labarai daga wurare daban daban za su sha banban,shi ya sa idan wurin hada lantarki bai dace ba,to,manema labarai ba za su gudanar da aiki lami lafiya ba.Muna kyautata aikinmu`

Shekarar da muke ciki wato shekarar 2007 ita ce shekara mai muhimmanci ga aikin shirya taron wasannin Olimpic na shekarar 2008,aikin ba da hidima ga kafofin watsa labarai na kwamitin shirya wasannin Olimpic yana samun kyautatuwa a kai a kai.Ko shakka babu,kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing zai cika alkawinsa wato zai samar da ayyukan zamani kuma zai samar da hidima mai kyau.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)


1 2