Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-11 08:27:34    
Kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing yana kokarin kyautata aikin hidima ga kafofin watsa labarai

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,kasar Sin ta taba yin alkawari ga kasashen duniya cewa,za ta shirya wani taron wasannin Olimpic mai siffar musamman a birnin Beijing,don tabbatar da wannan nufi,gwamnatin kasar Sin da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing suna sanya matukar kokari,kuma suna mai da hankali sosai kan aikin ba da hidima wajen watsa labarai.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Yayin da shekarar 2008 ke kara kusantowa,aikin share fage na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya shiga wani muhimmin mataki,alal misali,gine-ginen dakuna da filayen wasanni da gudanar da gasannin gwajin wasannin Olimpic,ban da wannan kuma,kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing yana kokarin kyautata ingancin aikin ba da hidima ga kafofin watsa labarai.

Saboda yawancin kafofin watsa labarai wadanda suka yi rajista domin halartar taron wasannin Olimpic na Beijing sun zo ne daga kasashen waje,wato sun kai kashi 95 cikin dari,don tabbatar da aikinsu lami lafiya a gun taron wasannin Olimpic,kwanakin baya ba da dadewa ba,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya fara gudanar da tsarin ba da hidima cikin sauri ga kafofin watsa labarai.Game da wannan,shugaban hukumar kula da kafofin watsa labarai na kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing Mr.Sun Weijia ya yi mana bayani cewa,  `Muna bin ka`idar ba da hidima mai kyau ga kafofin watsa labarai,an kafa tsarin ba da hidima cikin sauri ga kafofin watsa labarai a karkashin taimakon sassan da abin ya shafa na gwamnatin tsakiya da birnin Beijing.Daga nan za a samar da hidima ga dukkan kafofin watsa labarai na kasashen duniya daga dukkan fannoni a cikin sa`o`i 24 a kowace rana.`

1 2