Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-10 20:32:38    
Kasar Sin tana kokarin fama da bala'in ambaliyar ruwa a yankunan da ke tsakiyarta

cri

Ban da lardin Anhui, lardin Hubei da ke tsakiyar kogin Yangtse ma ya sha ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwariya. Tun daga ran 7 zuwa ran 8 ga wata, wurare da yawa na wannan lardi sun sha bala'un ambaliyar ruwa, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 tare da wasu mutane dubu dari 4 da suke shan bala'in. Wasu gidajen jama'a ma sun rushe sakamakon bala'in. Sabo da haka, hukumar jin dadin jama'a ta lardin Hubei tana kuma kokarin fama da bala'in domin tabbatar da samar wa jama'a abinci da ruwan sha da tufafi da wuraren kwana da likitoci da suke bukata.

Bisa labarin da cibiyar ba da labarin yanayin duniya ta kasar Sin ta bayar a ran 10 ga wata da safe, a cikin sa'o'i 24 masu zuwa, za a yi ruwa kamar da bakin kwaliya a yankunan gabashin birnin Chongqing da kudancin lardin Hubei da lardin Anhui da yankunan kudancni lardin Jiangsu. Hukumomin gwamnati na matakai daban-daban na kasar Sin za su kara mai da hankulansu kan bala'in ambaliyar ruwa, kuma za su dauki matakai iri daban-dabam domin fama da bala'in da tabbatar da jin dadin jama'a masu fama da bala'in. (Sanusi Chen)


1 2