Tun daga ran 28 ga watan Yuni, an samu bala'in ambaliyar ruwa mai tsanani a wasu lardunan da suke dab da kogin Huai da kogin Yangtse na kasar Sin sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwariya. Ya zuwa karfe 4 na yamma na ran 9 ga watan Yuli da muke ciki, yawan mutanen da suke fama da bala'in ya riga ya kai fiye da miliyan 20, ya kuma haddasa mutuwar mutane fiye da 100 tare da mutane fiye da 20 da suka bace a cikin bala'in.
Bayan aukuwar bala'in ambaliyar ruwan, babban ofishin ba da umurnin fama da bala'in ambaliyar ruwa da fari na kasar Sin da ma'aikatar jin dadin jama'a da kwamitin rage bala'u daga indallahi na kasar sun kaddamar da tsarin fama da bala'u daga indallahi cikin gaggawa, kuma sun aika da wasu rukunonin aiki zuwa yankuna masu fama da bala'in domin nuna jaje ga jama'ar da suke fama da bala'in da kuma ba da taimako ga yankuna wajen fama da bala'in. Mr. Pang Chenming, mataimakin direktan hukumar fama da bala'u daga indallahi ta ma'aikatar jin dadin jama'a ta kasar Sin ya gaya wa manema labaru cewa, "Muna yin namijin kokarinmu wajen nuna goyon baya ga yankuna masu fama da bala'in. Ya zuwa ran 10 ga watan Yuli, ma'aikatar jin dadin jama'a ta riga ta soma tsarin fama da bala'u daga indallahi har sau 14 tare da aikawa da rukunonin aiki na jin kai 12. A waje daya, an riga an kebe wa lardunan Anhui da Hubei da Sichuan da birnin Chongqing kudin Renminbi yuan miliyan 167 domin fama da bala'in."
Lardin Anhui da ke dab da kogin Huai da kogin Yangtse lardi ne da ke shan bala'in ambaliyar ruwa mafi tsanani a wannan karo. Wakilinmu Liu Jun da ke lardin Anhui ya gaya mana cewa, "Bisa sabuwar kididdigar da aka yi, yanzu mutane kimanin dubu 125 suna fama da bala'in ambaliyar ruwa a lardin Anhui. Yawan ruwan da ya yi ambaliya da aka fitar daga lardin ya kai kimanin cubic mita biliyan 1.53. Amma a ran 9 ga wata, hukumar nazarin yanayin duniya ta lardin Anhui ta sake ba da labari cewa, za a sake yin ruwan sama kamar da bakin kwariya a lardin."
A karkashin illar da ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwariya a yankunan da ke dab da kogin Huai, yawan ruwan da ke cikin dam din na Wangjiaba da ke kan kogin Huai yana ta karuwa. Sabo da haka, an riga an bude wata kafa domin gudanar ruwa da ke ambaliyar cikin unguwar Mengwa a ran 10 ga wata da yamma. Bugu da kari kuma, babban ofishin ba da umurnin fama da bala'un ambaliyar ruwa da fari na kasar Sin ya fara kaddamar da shirin fama da bala'in ambaliyar ruwa da ke kan matsayi na biyu tun daga ran 9 ga wata domin fama da bala'in ambaliyar ruwa a yankunan da ke dab da kogin Huai da tsugunar da jama'a masu fama da bala'in. Mr. Liu Jun ya bayyana cewa, "Hukumomin jin dadin jama'a na matakai daban-daban na lardin Anhui sun riga sun soma aikinsu na tabbatar da samar wa jama'a kayayyakin masarufi da manufofin jin kai. A waje daya, ana sufurin tantuna da sauran kayayyakin jin kai zuwa yankuna masu fama da bala'in ambaliyar ruwa cikin gaggawa. Wato, ana fama da bala'in ambaliyar ruwa bisa shirin da aka tsara kamar yadda ya kamata a lardin Anhui."
1 2
|