Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-10 17:36:18    
Kogin Wanquanhe na lardin Hainan

cri

Kogin Wanquanhe ya zama na uku a lardin Hainan saboda girmansa. Yana da mafari 2, mafarinsa na kudu shi ne gabashin babban tsaunin Wuzhishan, na arewa kuwa shi ne kudancin babban tsaunin Limushan. Wannan kogi mai tsawon misalin kilomita 160 ya ratsa gundumomi 4, fadin yankunan da ya shafa ya kai misalin murabba'in kilomita 1683. Akwai wata almara game da asalin wannan kogi. An ce, a can can can da, wasu dodo sun mamaye wannan yanki, Mutanen wurin sun sha wahalhalu sosai, shi ya sa sun yi ta kuka a duk rana da dare. Kukansu ya burgi gumakan da ke sararin sama. Wadannan gumaka sun canza hawayen da mutanen wurin suka fito da su da su zama dubban rafuka, sannu a hankali wadannan rafuka sun taru har ma sun zama wani babban kogi. Kogin ya nitsar da wadannan gumaka, ya jigilar su zuwa babban teku. Tun daga nan ne mutanen wurin sun fara kyawawan rayuwa cikin kwanciyar hankali, sa'an nan kuma an kira wannan kogi kogin Wanquanhe. Ma'anar Wanquan a Sinance ita ce dubban rafuka, 'He' kuwa shi ne kogi a Sinance.

Wurare masu ni'ima da aka samu a gabobin kogin Wunquanhe suna da kyan gani sosai, har ma ba a taba ganin irinsu a sauran wurare ba. A mafarinsa, masu yawon shakatawa suna iya kallon manyan tsaunakan da suka yi kama da hakoran zarto da kwazazabai da kwaruruwa marasa fadi da kuma ruwan da ke gagarowa, ya kuma yi kara kamar cida.

1 2