Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-09 18:25:26    
Ana gaggauta kau da cutar karacin sinadarin iodine a yammacin kasar Sin

cri

Chen Jixiang, mataimakin shugaban kungiyar cututtukan da su kan faru a wasu wurare na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekara ta 1994, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fara aiwatar da ka'idar kara sinadarin iodine a cikin gishiri don kawar da karancin sinadarin a duk fadin kasar, wadda ta samu sakamako mai kyau sosai. Kuma ya kara da cewa, "A shekara ta 1995, kasar Sin ta fara aiwatar da ka'idar kara sinadarin iodine a cikin gishirin da fararen hula su kan ci, kuma a wancan lokaci, yawan gishirin da ke da sinadarin iodine ya kai kashi 30 cikin dari kawai, amma yanzu wannan jimla ta riga ta kai fiye da kashi 90 cikin dari."

Ko da yake ayyukan shawo kan cututtukan karancin sinadarin iodine na kasar Sin sun samu ci gaba sosai, amma ana kasancewar matsalolin da ba a iya kyale su ba. Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Wang Longde ya jaddada cewa, a wasu yankunan kananan kabilu da kuma wadanda da ke da wuyar zuwa na kasar Sin, ya kamata a dora muhimmanci kan batun rashin samun isasshen gishirin da ke da sinadarin iodine. Musamman ma a lardunan Gansu da Qinghai da jihar Xinjiang da dai sauran larduna 4 na yammacin kasar Sin, gundumomi kusan 400 suna fuskantar barazanar karancin sinadairn iodine. Sabo da haka, dole ne a kara mai da hankali sosai kan yammacin kasar Sin, idan ana son tabbatar da cimma burin kau da cututtukan karancin sinadarn iodine a garuruwa fiye da 95 cikin dari na duk fadin kasar a shekara ta 2010.

A watan Agusta na shekarar da ta gabata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta shirya kwararru wajen yin bincike kan halin karancin sinadarin iodine da jihar Xinjiang ke ciki. Daga baya kuma an gano cewa, fiye da rabi dag cikin manoma da makiyaya na wurin suna cikin halin karancin sinadarin iodine sakamakon rashin cin gishirin da ke da sinadarin.

Shugaban hukumar kiwon lafiya ta jihar Xinjiang Mamatimin Yasen ya nuna cewa, "jihar Xinjiang, musamman ma gwamnatocin wurare da hukumomin da abin ya shafa na yankunan da ke fama da cututtukan karancin sinadarin iodine na lardin sun kara tabbatar da ayyukansu wajen kawar da cututtukan. Kuma an tsai da kudurin samar da kudade Yuan miliyan 18 ga manoman da ke shiyyar Sidi ta kudancin jihar Xinjiang wajen cin gishirin da ke da sinadarin iodine, da kuma kebe kudade Yuan miliyan 2.5 ga gwamnatin jihar wajen gudanar da ayyukansu, ta yadda za a iya ba da tabbaci sosai a fannin manufofi domin cimma burin kau da cututtukan karancin sinadarin iodine a shekara ta 2010." (Kande Gao)


1 2