Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-09 18:25:26    
Ana gaggauta kau da cutar karacin sinadarin iodine a yammacin kasar Sin

cri

Sinadarin iodine wani irin sinadarin gina jiki ne da dan Adam yake bukata. Idan babu isasshen sinadarin iodine a jikin dan Adam, to za a kamu da cututtuka iri daban daban kamar cutar makoko da rashin samun bunkasuwar basira kamar yadda ya kamata da dai sauransu. Kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da ke fuskantar barazanar karancin sinadarin iodine, an taba samun bullar cututtukan karancin sinadarin iodine a yawancin lardunan kasar. Amma bayan da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta fara daukar matakai iri daban daban a shekaru 80 na karnin da ya gabata, an samu sakamako mai kyau wajen kawar da cututtukan karancin sinadarin iodine.

A tsakiyar watan Mayu na shekarar da muke ciki, ma'aikatar kiwon lafiya da kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare da kuma babban kamfanin kula da gishiri na kasar Sin sun kira taron kara wa juna ilmi kan tsara manufofin shawo kan cututtukan karancin sinadarin iodine a birnin Urumqi, hedkwatar shiyyar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kai a kasar Sin. Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Wang Longde ya bayyana cewa, "Sakamakon dan kwarya-kwaryar bincike na karo na biyar da aka gudanar kan cututtukan karancin sinadarin iodine a shekara ta 2005 da kuma binciken da aka gudanar kan gishirin da ke kunshe da sinadarin iodine a dukkan garuruwan kasar Sin a shekara ta 2006 ya bayyana cewa, yawan sinadarin iodine da ke cikin jikin mutanen kasarmu ya yi daidai, kuma yawan gishiri mai inganci da ke kunshe da sinadarin iodine da jama'a suke ci, da yawan yaran da ke fama da cutar makoko, da kuma yawan sinadarin iodine da ke cikin fitsarin mutane dukkansu sun kai ma'aunin kawar da cututtukan karancin sinadarin iodine na kasa da kasa. Kuma wannan ya shaida cewa, aikin kawar da cututtukan na kasarmu yana kan gaba a duk duniya."

1 2