Kwararru sun nuna cewa, yayin da muke jin matukar farin ciki da gano sabon filin man fetur, wajibi ne, mu fahimci sosai cewa, ya kamata, kasar Sin ta nace ga raya makamashi da tsiminsa. Malam Zhang Zhonghua na cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum ta kasar Sin ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin ke bunkasa harkokin tattalin arzikinta, tsimin makamashi manufa ce da take ta neman cimma a kullum. Ya ce, " wajibi ne, mu yi kokari wajen ci gaba da tsimin makamashi, da rage yawan makamashi da muke amfani da su, mu kiyaye muhalli, mu rage abubuwa masu gurbacewar muhalli da muke fitarwa. Gano sabon babban filin man fetur na Nanpu ba zai canja manufar da muke bi game da raya zaman al'umma mai tsimkin makamashi."
Bisa shirin da aka tsara, za a hako gurbataccen man fetur tan miliyan 10 daga filin man fetur na Jidong a duk shekarar badi. A kwanan baya, jami'in filin sun dauki alkawari cewa, nan gaba za su hada kansu da kamfanonin kasa da kasa wajen hako gurbataccen man fetur ta hanyar zamani, ta yadda za su cim ma manufar rashin fitar da abubuwa masu gurbacewar muhalli ko kiris. (Halilu) 1 2 3
|