A kwanakin baya, kamfanin man feter da gas na kasar Sin ya sanar da cewa, an gano wani babban filin man fetur mai suna "Jidongnanpu" wanda ke da gurbataccen man fetur sama da tan biliyan 1 da miliyan 2 a bakin teku na Bohai na lardin Hebei da ke a arewacin kasar Sin. Bayan haka wannan sabon filin man fetur da aka gano ya jawo hankulan jama'ar Sin da ta duniya kwarai.
Mashigin teku na "Bohai" yana daya daga cikin wurare mafi arzikin man fetur da gas a kasar Sin. Wannan sabon babban filin man fetur da aka gano wani filin man fetur ne mai arziki da inganci wanda ba safai a kan iya samunsa ba. Haka kuma wannan filin man fetur fili ne mai girma da aka gano a kasar Sin cikin shekaru sama da 30 da suka wuce.
An fara yin binciken man fetur a wuri mai suna "Nanpu" da ke a bakin teku na Bohai ne a shekarar 1993. Kamfanin filin man fetur na Jidong na kasar Sin wanda ke mallakar filin man fetur na Nanpu ya taba hadin kansa da shahararrun kamfanonin man fetur na kasashen waje guda biyu, don binciken gurbataccen man fetur a wurin, ko da yake sun shafe shekaru 7 ko 8 suka yin binciken cikin hadin guiwarsu, amma ba su gano man fetur mai yawa ba.
1 2 3
|