Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-04 15:51:56    
Wata shaharariyar zabiya ta kasar Sin mai suna Mayila

cri

An haifi zabiya Mayila ta kabilar Kazak a wani gidan mawaka da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, sunanta ya yi daidai da na wata shaharariyyar wakar jihar Xinjiang, wato Mayila ke nan. Zabiya Mayila ta gaya wa manema labaru cewa, iyayena dukkansu suna aikin wake-wake da kide-kide, wato mahaifina yana tsara kide-kide, mahaifiyata ita ma zabiya ce. A lokacin da nake karama, na yi kuka da babbar murya, saboda haka iyayena sun ce, wata zabiya daban ce da aka haife ta, kuma zan yi gadonsu ba shakka ko kadan. Mahaifina ya kuma gaya mini wani labari dangane da wata shaharariyyar wakar da aka rada mata suna cewar wai "Mayila", kuma mahaifina ya rada mini wannan suna, wato Mayila ke nan. Tun lokacin da na ke karama, na kan saurarar wakar nan, kuma na sami girma tare da saurarar wakar. Bayan da na balaga, ni ma ina rera wakar har zuwa yanzu.

Tun da nake karama, ina da sha'awa sosai da rera wakoki bisa sanadiyar tallafin da iyayena suka yi mini. A lokacin da na cika shekaru 8 da haihuwa, sai na soma koyon kada Piano a wajen mahaifina, a shekarar 1982, na shiga kolejin koyon fasahohin nuna wasanni na Yili na jihar Xinjiang don koyon kada Piano. A shekarar 1984, ya je karatu a sashen wake-wake da kide-kide na jami'ar kabilu ta tsakiya ta kasar Sin don koyon ilmin rera wakoki. A shekarar 1987, karo ne na farko da na shiga gasar rera wakoki tare da samun lambar yabo, A shekarar 1988, zabiya Mayila ta sauka karatu a jami'ar kabilu ta tsakiya ta kasar Sin, kuma ta zama malamar koyarwa a jami'ar, a Shekarar 2002, bisa gayyatar da babban gidan nuna wasannin kwaikwayo tare da wake-wake da kide-kide na kasar Faransa ya yi mata ne, zabiya Mayila ta yi kwangilar nuna wasanni da gidan cikin shekaru uku, abin da ba a iya manta da shi ba shi ne babbar 'yar wasan da ya yi a cikin wasan da ake kira " soyayya mai dadi", zabiya Mayila ta bayyana cewa, na zama 'yar wasa mai suna Adina a cikin wasan "soyayya mai dadi", dukkan 'yan wasan suna nuna wasanni tare da nuna abu mai ban dariya sosai, a duk lokacin da aka kawo karshen nuna wasan, 'yan kallon wasan ba su son tashi daga wurin nuna wasan ba. Daga nan, sai na kara samun suna sosai a duniya.

Bisa matsayin mitumiyar da ke girma da samun tarbiyya a gabashin duniya, Mayila ta nuna wasanni a dakalin kasashen yamma, ko shakka babu ta yi kokari sosai da sosai. Da farko, dole ne ta koyi harsunan kasashen waje, kullum tana gwada muryarta ba tare da kasala ba, kuma dole ne tana kasancewa cikin hali mai kyau sosai wajen nuna wasanni, Mayila ta ce, ba abin sauki ba ne gare ta. Ta ce,tamkar yadda 'yan wasan motsa jiki suka yi, in wata rana ban yi kokari ba, to ni kaina na iya sanin abu maras kyau da na yi, in kwana biyu ban yi kokari ba, to wanda ke kusa da ni ya iya fahimtar cikas da na samu, in kwanaki uku da ban yi kokari ba, sai 'yan kallo suka fahimci matsalolin da suka same ni. Kai , Kullum hakan nake yi, a gaskiya dai na gaji sosai.


1 2