A lokacin da masu yawon shakatawa suke yawo a cikin gandun daji, suna iya ganin cewa, ganyayyen itatuwa sun ba da kariya daga rana, manyan bishiyoyi sun mike a sama, sa'an nan kuma, hawa da gangarar da ke nan su kan faranta zukatan masu yawon shakatawa. In masu yawon shakatawa suka hangi nesa daga kololuwar babban tsaunin Wuzhishan, to, sun fahimci cewa, tekun gajimare sun fito ne daga karkashin kafafunsu, sun iya yawo a cikin sararin sama.
A lokacin da ake rana, kuma babu gajimare a sararin sama, mutane suna iya kallon kyawawan teku da kananan tsibirai daga kololuwar babban tsaunin. Masu yawon shakatawa suna iya ganin fitowar rana tare da hasken rana mai launin zinariya da sassafe, haka kuma, sun iya more idanunsu da faduwar rana da dare, a lokacin can dukkan sararin sama da teku sun kasancewa mai launin ja.
Dabbobi da tsuntsaye da tsire-tsire masu daraja kuma masu yawa suna zama a cikin gandun dajin nan. Saboda haka ne gandun daji da ke babban tsaunin Wuzhishan wuri ne mai kyau a fannonin yawon shakatawa da yin tafiya mai ban mamaki da kuma gudanar da harkokin nazarin kimiyya.(Tasallah) 1 2
|