Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-03 15:51:58    
Babban tsaunin Wuzhishan a lardin Hainan

cri

Ma'anar Wuzhi a Sinance ita ce yatsu 5 na mutum. Dalilin da ya sa ake kiran wannan babban tsauni da sunan Wuzhishan shi ne domin godiya ga dogon lokaci na zaizaiyar kasa, kololuwar babban tsaunin sun yi kama da hakoran zarto, sun yi kama da yatsu 5 na mutum. Babban tsaunin Wuzhishan babban tsauni ne mafi tsayi a lardin Hainan na kasar Sin, an mayar da shi tamkar alamar Hainan, shi ne kuma daya daga cikin shahararrun manyan tsaunuka a kasar Sin.

Babban tsaunin Wuzhishan yana cikin kudu maso yammacin gundumar Qiongzhong. A cikin dukkan yatsu 5 na babban tsaunin Wuzhishan, yatsa na 2 mai tsayin misalin mita 1,867 ya fi saura 4 tsayi, sa'an nan kuma, ya fi babban tsaunin Taishan tsayi har da misalin mita 343. Yatsa na 3 da na 4 da na 5 suna hade da juna, amma ko wanensu yana matsayin kansa. A idanun masu yawon shakatawa, wannan na da kyan gani sosai kuma mai ban mamaki.


1 2