Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-26 17:41:49    
Shan shayi zai ba da taimako wajen rage damuwar tunani

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan shayi zai ba da taimako wajen rage damuwar tunani, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, an fara horar da malamai mata na kauyuka a jihar Sichuan ta kasar Sin. To, yanzu ga bayanin.

Kowa ya sani, shayi yana kunshe da sinadarin caffein, shi ya sa shan shayi zai iya wartsakar da mutane. Haka kuma sabo da shayi yana kunshe da wani sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant, shi ya sa yana iya ba da taimako sosai wajen sake jikin mutum. Amma bisa wani nazarin da kasar Birtaniya ta yi a 'yan kwanakin da suka gabata, an ce, shan shayi zai ba da taimako wajen rage damuwar tunani.

Bisa labarin da kamfanin watsa labarai na kasar Birtaniya ya bayar, an ce, masu ilmin kimiyya na jami'ar London ta kasar sun gano cewa, shan shayi zai iya ba da taimako wajen rage yawan sinadarin hormone mai kawo damuwar tunani da ke cikin jikin mutum, shi ya sa mutanen da su kan shan shayi sun fi saukin rage damuwar tunani idan an kwatanta su da wadanda su kan sha lemo.

Manazarta sun kasa samari maza 75 da su kan sha shayi cikin kungiyoyi biyu, da kuma gudanar da wani bincike na tsawon makwanni shida gare su. Domin magance kuskuren sakamakon binciken sakamakon tasirin da launi da kamshin shayi su kan bai wa masu shiga binciken, manazarta sun yi amfani da abin sha da ke da launin shayi a maimakon shayi na gaskiya. Mutanen da ke cikin rukuni daya sun sha irin wannan abin sha da ke kunshe da sinadarin da ke cikin shayi, amma mutanen da ke cikin dayan rukunin sun sha irin wannan abin sha da ke da kamshin shayi amma ba tare da sinadarin da ke cikin shayi ba.

1 2