Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-26 10:27:09    
Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin ya yi magana a kan batun Darfur

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron, Babban sakataren Majalisar Dinkin duniya Mr Ban Ki Moon ya kuma takaita ra'ayi daya da wakilan bangarori daban daban suka samu, wato na farko, samar da taimakon jinkai ga shiyyar Darfur; Na biyu, jibge rundunar sojojin da ke hada da na Majalisar Dinkin duniya da na kungiyar tarayyar kasashen Afrika a shiyyar, Na uku, mai da hankali kan batun raya kasar Sudan cikin dogon lokaci; Na hudu, ciyar da ayyukan daidaita batun Darfur ta hanyar siyasa gaba , wannan yana daya da matsayin bangaren kasar Sin.

Kwana baya, wasu kafofin yada labarai da wasu 'yan siyasa na kasashen yamma sun kai suka ga gwamnatin kasar Sin ba gaira ba dalili, sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta shiga aikin daidaita batun Darfur tare da himma ba, game da wannan Mr Liu Gui ya karyatar da cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da gudumuwarta wajen sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur, musamman ma gwamnatin kasar Sin ta shawo kan kasar Sudan ta yadda kasar ta karbi shirin Mr Kofi Annan game da daidaita batun ta matakai uku. A ranar 12 ga watan Yuni, an bayar da hadadiyyar sanarwa a tsakanin bangarori uku a birnin Addis ababa, a cikin sanarwar, kasar Sudan ta amince da shirin Mr Annan ba tare da kowane sharadi ba.(Halima)


1 2