Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-26 10:27:09    
Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin ya yi magana a kan batun Darfur

cri

A ranar 25 ga wannan wata, an kira taron duniya kan batun Darfur na kasar Sudan a birnin Paris. Kasashen Amurka da Britaniya da Faransa da Sin da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar tarayyar kasashen Turai da Kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da Bankin duniya da Bankin raya kasashen Afrika da sauran kungiyoyin kasa da kasa sun tura wakilansu don halartar taron. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr Ban Ki Moon ya nuna babban yabo ga gwamnatin kasar Sin bisa sakamakon kokari da gudumuwa da ta yi a kan batun. A lokacin gudanar da taron, wakilin gidan rediyo kasar Sin ya ziyarci wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin Mr Liu gui a kan batun Darfur, inda ya ce, babban makasudinmu na halartar taron shi ne don musanya ra'ayoyi a tsakaninmu da gamayyar kasa da kasa a kan daidaita batun Darfur ta hanyar siyasa da kuma saurarar ra'ayoyi daga bangarori daban daban. A sa'I daya kuma, don bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali da yin lura sosai kan batun.

Kullum gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga batun Darfur. A watan Janairu da watan Afril na shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta tura mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin Mr Zhai Jun zuwa kasar Sudan don yin ziyara. A watan Mayu, gwamnatin kasar Sin ta nada dan diplomasiya Mr Liu Gui wanda yake da cancantar matsayi wajen harkokin waje don ya zama wakilin musamman a kan batun Darfur. Sa'anan kuma, Mr Liu Gui ya je shiyyar Darfur har sau biyu don yin bincike da kuma yin shawarwari da shugabannin kasar Sudan, har ma ya tafi tare da hakikanin alkawarin gwamnatin kasar Sin da taimakonta. Ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsai da cewa, a watan Augusta, bisa bukatun Majalisar dinkin duniya ne, za ta tura rassan rundunar sojojinta da yawansu ya kai 275 wadanda suke da sana'o'I iri iri da yawa. A sa'I daya kuma, mun riga mun samar wa shiyyar Darfur taimakon agaji da darajarsa ya kai kudin Amurka dolla dubu 10, sa'anan kuma mun himmantar da kamfanonin kasar Sin da ke kasar Sudan don kara samar da taimakon agaji, Mr Liu Gui ya kuma ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin ta tura kungiyar kwararrunta ba da dadewa ba. Za mu kafa cibiyar ba da misali ga samar da fasahohin noma na kasar Sin a kasar Sudan, a sa'I daya kuma, kamfanoni masu jarin kasar Sin za su shiga ayyukan ruwa na kasar Sudan don samar da ruwan sha ga shiyyar Darfur.

1 2