Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-25 18:39:30    
Hong Kong na daya daga cikin wuraren duniya da ake fi gudanar da harkokin tattalin arziki ba tare da shinge ba

cri

Bayan dawowar Hong Kong a kasar Sin ba da dadewa ba, rikicin kudi na Asiya ya kama Hong Kong. Tun daga kwanaki 10 na tsakiya na watan Yuni na shekarar 1997 zuwa watan Agusta na shekarar 1998, 'yan kasuwa na kasashen duniya sun tallata kasuwanin takardun hada-hadar kudi da musayar kudi na Hong Kong. Hukumar Hong Kong ta shigar da musayen kudin da ta ajiye cikin kasawannin, a karshe dai ta ci nasara. Wasu suna ganin cewa, wannan ya nuna cewa, hukumar Hong Kong ba za ta ci gaba da bin tsarin tattalin arziki na kasuwanci ba. Amma shugaba Joseph C. K. Yam na hukumar harkokin kudi ta Hong Kong ya yi hasashen cewa,'Tsarin tattalin arziki na kasuwanci na da kyau sosai. Amma sakamakon da muka samu daga wajen daidaita rikicin kudi na Asiya a shekarar 1997 zuwa ta 1998 shi ne ana iya sarrafawar kasuwanni da ya ga dama a sakamakon bin irin wannan tsari, shi ya sa muna bukatar sa ido kan wadannan kasuwanni a tsanake. In wasu suna yunkurin sarrafa kasuwannin, to, za mu dauki matakai, za mu bi ka'idojin kasuwannin.'

A cikin rahoton da gidauniyar Heritage ta kasar Amurka da jaridar The Wall Street Journal ta kasar suka bayar a kwanan baya game da ma'aunin tafiyar da harkokin tattalin arziki ba tare da shinge ba a shekarar 2007, an zabi Hong Kong a matsayin wurin da ke fi samun 'yancin kai wajen gudanar da harkokin tattalin arziki a tsakanin wurare 157 na dun duniya. Wannan ne karo na 13 a jere da gidauniyar Heritage ta kasar Amurka ta bai wa Hong Kong wannan girmamawa.

Gwamnan hukumar Hong Kong Donald Tsang Yam-kuen ya ce, dawowar Hong Kong a kasar Sin ba ta kawo illa ga Hong Kong a fannin gudanar da harkokin tattalin arziki ba tare da shinge ba. Ya ce,'A maimakon samun raunannawa, a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, 'yancin kai da mu jama'ar Hong Kong ke so da dokokin da muke mai da hankulanmu a kai da zaman al'ummar kasa mai adalci da kudin da muke amfani da shi da kuma ko wane abu sun sami kyautatuwa.'(Tasallah)


1 2