Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-25 18:39:30    
Hong Kong na daya daga cikin wuraren duniya da ake fi gudanar da harkokin tattalin arziki ba tare da shinge ba

cri

Hong Kong ta yi suna ne a duniya domin mallakar tasoshin jiragen ruwa, inda ake shiga da kuma fitar da kayayyaki ba tare da biyan harajin kwastan ba, ita ce kuma daya daga cikin wuraren duniya da aka fi samun nasara wajen gudanar da tsarin tattalin arziki na kasuwanci. Bisa abubuwan da ke cikin babbar doka ta yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, an ce, bayan dawowarta a karkashin shugabancin kasar Sin, har zuwa yanzu Hong Kong tana aiwatar da tsarin tattalin arziki na kasuwanci na jari-hujja. A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, a karkashin tsarin 'kasa daya, amma tsarin mulki biyu', har zuwa yanzu dai Hong Kong na daya daga cikin wuraren duniya da aka fi gudanar da harkokin tattalin arziki ba tare da shinge ba.

Tun bayan da aka bude tasoshin jiragen ruwa a Hong Kong a shekara ta 1841, Hong Kong tana bin manufar shigi da ficin kayayyaki ba tare da biyan harajin kwastan ba. Irin wannan manufa ta jawo 'yan kasuwa da kyayyaki daga wurare daban daban na duniya, haka kuma ta sa kaimi kan yin cudanya a tsakanin babban yankin Sin da wurare daban daban na duniya a fannonin tattalin arziki da ciniki. Zaunannen wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma shahararren mai masana'antu na Hong Kong malam Tsang Hin-Chi ya bayyana cewa,'Bayan da kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen duniya, ta raya tattalin arzikinta sosai, shi ya sa ta sayar da kayayyaki zuwa kasashen duniya ta hanyar tasoshin jiragen ruwa na Hong Kong.'

Domin dacewa da manufar shigi da ficin kayayyaki ba tare da biyan harajin kwastan ba, Hong Kong tana aiwatar da tsarin tattalin arziki na kasuwanci. Bayan dawowarta a kasar Sin, Hong Kong ba ta canza irin wannan tsarin tattalin arziki ba. Babbar doka ta Hong Kong ta kayyade cewa, ana ci gaba da bin manufar shigi da ficin kayayyaki ba tare da biyan harajin kwastan ba. Ba za a buga harajin kwastan ba, sai dai an tanadi sauran ka'idoji a cikin shari'a. Sa'an nan kuma, Hong Kong tana aiwatar da manufar yin ciniki ba tare da shinge ba, ta kuma tabbatar da rarraba kayayyaki da dukiyoyi da jari-hujja a zahiri ba tare da shinge ba. Ana aiwatar da wadannan ka'idojin da abin ya shafa yadda ya kamata. Mataimakin shugaban hukumar raya ciniki ta Hong Kong Alan Wong ya ce,'Hong Kong ba ta taba yin sauye-sauye a wannan fanni ba, tana dogara da tsarin tattalin arziki na kasuwanci. Irin wannan tsari ne ya taimake mu domin samun bunkasuwa. Hong Kong ta mai da hankali sosai kan wannan fanni.'

1 2