Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-15 12:33:15    
Mene ne makomar batun nukiliyar Iran

cri

A zahiri dai, gwamnatin Iran ta rigaya ta rage hadin gwiwar da take yi tare da hukumar kula da makamashi ta duniya. A 'yan kwanakin baya, gwamnatin Iran ta yanke shawarar yin watsi da binciken da sufetocin hukumar kula da makamashi ta duniya suke son yi ga manyan na'urorin sarrafa sinadarin Uranium yayin da take kin bayar da bayanan da abin ya shafa game da sabbin gine-ginen nukiliyarta.

An kuma labarta ,cewa shekaranjiya, shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya sake nanata ,cewa yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, wani hakki ne da ya kamata dukannin jama'ar Iran su samu. ' Komai matsin da za a kai mata', in ji shi, 'Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na mallakar nukiliya ba'. Ban da wannan kuma, shugaba Ahmadinejad ya ce, tarihi ya rigaya ya shaida, cewa kudurorin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar ba su da amfani ga Iran. Ko da wasu kasashe masu ci gaban masana'antu na Yamma sun garkama sabon takunkumi kan Iran ta kwamitin sulhun, babu tantama ba za su cimma burinsu ba.

A ganin Mr. Baradei, halin da ake ciki yanzu yana kasa yana dabo. Amma ya furta, cewa har wa yau dai, akwai lokacin daidaita maganar nukiliyar Iran ta fuskar diplomasiyya domin Iran za ta dauki shekaru 3 zuwa 8 ne wajen kera wani atom bom.

A lokaci daya, Mr. El Baradei ya ja kunnen kasashen Amurka da Isra'ila don kada su warware batun nukiliyar Iran ta hanyar yin amfani da karfin soji. Ya ce, idan sun kai wa Iran hari, to wannan dai zai kasance tamkar " mahaukacin mataki" ne da za su dauka.

Ra'ayoyin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, warware batun nukiliyar Iran ta hanyar yin shawarwari, wata hanya ce mafi kyau da za a bi domin hakan yana amfana wa kiyaye zaman lafiya da kuma zama mai dorewa na Gabas ta Tsakiya da kuma fadin duk duniya. ( Sani Wang )


1 2