Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-15 12:33:15    
Mene ne makomar batun nukiliyar Iran

cri

An labarta, cewa jiya Alhamis, babban daraktan hukumar kula da makamashi ta duniya Mohammed El Baradei ya yi kira ga gwamnatin Iran da ta dakatar da shirin habaka matakin inganta sinadarin Uranium. Cewa ya yi hakan zai iya sassauta rikici da ake yi sakamakon fargabar da gamayyar kasa da kasa suke yi ga yunkurin Iran na kera makaman nukiliya. Amma a nasa bangaren, wakilin din-din-din na Iran dake wakilci a hukumar kula da makamashi ta duniya Ali Asghar Soltanieh ya fadi, cewa Iran ta kasance wata kasa ce dake da fasahar inganta sinadarin Uranium. ' Saboda haka', in ji shi, ' lallai lokaci ya wuce da za a datakar da harkokin inganta sinadarin Uranium cikin gajeren lokaci'. A sa'i daya kuma, yanzu gwamnatin Amurka tana gaggauta yin harkoki domin ganin an zartar da sabon kudurin kara garkama wa Iran takunkumi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. To, mene ne makomar batun nukiliyar Iran ? Gamayyar kasa da kasa na sake mai da hankali da kuma nuna damuwa a kai.

Mohammed Baradei ya furta, cewa yanzu kasar Iran ta rigaya ta harhada na'urorin inganta sinadarin Uranium da yawansu ya kai 1,700 zuwa 2,000. Ana kuma kyautata zaton cewa zai kai 3,000 a karshen wata mai kamawa. Lallai alkaluman sun yi yawa. Mr. Baradei ya bayyana, cewa idan Iran ba ta so ta yi shirin kera makaman nukiliya, to abun ba zai zama wajabi ba ta habaka matakin inganta sinadarin Uranium cikin gaggawa. Amma duk da haka, Mr. Baradei ya ce, idan gwamnatin Iran ta dakatar da kerawa da kuma harhada sabbin na'urorin inganta sinadarin Uranium tun daga yau, to wannan zai zama mataki na farko ne da ta dauka don warware rikicin.

Amma fa, bangaren Iran bai mayar da martani mai yakini kan furucin El Baradei ba. Ali Soltanieh ya fada wa kafofin yada labarai, cewa kasar Iran ta kasance wata kasa ce dake da fasahar inganta sinadarin Uranium, wajibi ne gamayyar kasa da kasa su amince da hakikanin abu. Ya kuma jaddada, cewa ya kamata a warware maganar nukiliyar Iran cikin muhimman tsare-tsare na hukumar kula da makamamshi ta duniya. ' shiga tsakani da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke yi' a cewar sa, ' ba zai haifar da komai ba illa zai janyo hali mai sarkakiya'. Ya kuma kara da cewa, idan kwamitin sulhun ya fito da sabon kudurin garkama takunkumi, to labuddah Iran za ta rage hadin gwiwar da take yi tare da hukumar kula da makamashi ta duniya.

1 2