Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-14 20:34:56    
Halin da kasar Sin ke ciki a fannin yawan mutane

cri

Gwamnatin kasar Sin ta nace ga bin manufar hada batun yawan mutane da batun samun bunkasuwa,ta mai da batun karuwar yawan mutane cikin babban shirinta na bunkasa tattalin arziki da samun cigaban zamantakewa,ta yi iyakacin kokarinta wajen neman samun daidaito kan karuwar yawan mutane da cigaban tattalin arziki da zaman jama'a,karuwar yawan mutane ta dace da yadda ake amfani da albarkantan kasa da kuma kiyaye muhalli.Tun daga shekaru casa'in na karni na 20,a kowace shekara gwamnatin kasar Sin ta kira tarurruka kan yawan mutane da albarkantan kasa da kuma muhalli,ta yi la'akari da batutuwa da dama ta kuma yi shirye shiryen daidaituwa,ta kuma kinkintsa mutanenta da kuma dauki matakai wajen dokoki da wayar da kai da kuma tattalin arziki da hukumomi wajen warware matsalar yawan mutane,ta hada da ayyukan raya tattalin arziki da kayyade yawan haihuwa da baza ilimi da inganta lafiyar jama'a da yaki da talauci da tabbatar da zaman jin dadin jama'a da inganta matsayin mata da kafa iyalai masu wayewar kai da zaman jin dadi gu daya.A shekara ta 2003,ta canza sunan kwamitin kasa kan kayyade yawan haihuwa zuwa kwamitin kasa mai kula da ayyukan yawan mutane da kayyade haihuwa ta yadda za a kara nazarin batun karuwar yawan mutane da tsara shirin karuwar mutane ta hanyar kimiyya.A farkon shekara ta 2004,gwamnatin kasar Sin ta kinkintsa kwararru na fannoni da dama da su fara nazarin shirin karuwar mutanen kasa,sun yi nazarin batutuwa na yawan mutane da ingancinsu da sassansu da kuma yadda suke kasancewa da kuma canje canjen da aka samu a fannin nan da kuma dangantaku tsakanin tattalin arziki da zamantakewa da albarkatun kasa da muhalli.Wajen nazarin shirin karuwar yawan mutanen kasa an kawo wata shawara cewa kamata ya yi a ba da fiffiko a fannin inganta mutane da mai da kasar Sin mafi yawan mutane kasa da za a fi samun kwararru.Wannan shawara ta ba da taimako ga kasar Sin wajen tsara shirin matsakaicen lokaci na karuwar yawan mutane da babban shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da cimma daidaito tsakanin yawan mutane da tattalin arziki da zamantakewa da albarkatun kasa da kuma muhalli da kuma samun dauwamamen cigaba.

A ran 9 ga watan Fabriru na shekara ta 2006,majalisar gudanarwa ta gwmnatin kasar Sin ta bayar da wani shirin raya kimiyya da fasaha na matsakaici da dogon lokaci (wato daga shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2020) na kasa,wanda a ciki ta bayyana makasudinta kan yawan mutane a cikin shekaru sha biyar masu zuwa,da yawansu ba zai wuce miliyan dubu da dari biyar ba.Wani matakin da ta dauka wajen karuwar yawan mutane da inganta lafiyarsu shi ne kayyade yawan haihuwa da inganta jariran da aka haifa.Za a sa ido kan harkokin haihuwa da samar da dabaru da magunguna da injunan asibiti da kuma abinci mai gina jiki wajen hayayyafa,ta haka za a ba da tabbacin kimiyya wajen samun karuwar yawan mutanen kasa ba zai zarce miliyan dubu da dari biyar ba da nakasasu jarirai da za a haifa ba za su wuce kashi uku cikin kashi dari na daukacin jarirai ba.

Wani mataki dabam da za a dauka wajen tabbatar da wannan manufa shi ne dora muhimmanci kan rigakafin cututtuka.gwamnatin kasar Sin ta dukufa kain da nain wajen yin rigakafi,ta mai da hankali wajen inganta lafiyar jama'a da magance cututtuka,ta yi nazarin hanyoyin da za a bi wajen rigakafi da kuma gano sanadin cututtuka tun da wuri,ta kuma kara kwarewar masu aikin jiyya nata wajen gano sanadin cututtuka da warkar da su,ta kuma hada likitancin gargajiya na kasar Sin da likitanci na kasashen yamma,ta rika sabunta hanyoyin kiwon lafiya da ake bi a kasar Sin da su zama na zamani a duniya.tana kokarin kafa cikakken tsarin ba da magani na gargajiya na kasar Sin da hanyoyin da ake bi ta kimiyya,ta gaji abubuwa masu nagari da likicin gargajiya na Sin ya kunsa.ta kuma sa kaimi waen bunkasa masana'antun hada magungunan gargajiya na kasar Sin da kirkiro sabbin magunguna da samar da na'urori na zamani wajen kiwon lafiya.Haka kuma ta kokarta wjen samo sabbin hikimomi da fasahohin hada sabbin magunguna da samar da injuna da na'urorin da ake bukata a asibiti da sauran kayayyakin ta haka kuwa za a kafa cikakken tsarin jiyya a duk fadin kasar Sin da samo fasahohin hada sabbin magunguna da na'o'rorin da ake bukata a asibiti.

A cikin shirin,an kuma tanadi cewa kayyade yawan haihuwa da inganta jariran da aka haifa da kuma rigakafin manyan cututtuka,mataki ne da ya wajaba a dauka wajen kafa zamantakewa mai jituwa.kayyade yawan haihuwa da inganta mutane da kyautata lafiyar mutanen kasa dukkansu suna bukatar taimakon kimiyya da fasaha.sabili da haka aka kawo shawarar yin amfani da roba wajen jima'I da magance haifar nakasassu da magance cututtuka a fannin zuciya da kwalkwalwa da jijiniya da ciwon kanjiki da sauran cuttuka,haka kuma za a sanya kokari wajen magance cututtuka da aka fi gani a birane da karkara da cin gadon likitancin gargajiya na kasar Sin da sabunta shi,dukkan wadannan muhimman batutuwa da ya kamata a sa hankali a kai.

Jama'a masu sauraro,kun dai saurari shirinmu na Me Ka Sani Game da Kasar Sin.wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau.sai wannan lokaci a mako mai zuwa.(Ali)


1 2