Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-14 20:34:56    
Halin da kasar Sin ke ciki a fannin yawan mutane

cri

Jama'a masu sauraro assalam alaikun,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a wannan shirin Me Ka Sani Game da Kasar Sin.A cikin shirinmu na yau za mu dan gutsura muku wani bayani kan yawan mutanen kasar Sin.

Kasar Sin kasa ce mai tasowa wadda ta fi yawan mutane a duniya.Mutanenta sun yi yawa amma albarkatan kasa ba su yi yawa ba,halin da take ciki bai kai yadda take bukata ba,wannan ainihin hali ne da kasar Sin ke ciki a halin yanzu,da wuya a canza wannan hali cikin kankane lokaci.Matsalar yawan mutane matsala ce da kasar Sin ke fuskanta cikin dogon lokaci a mataki na farko na raya zaman gurguzu,kuma ta kasance muhimmiyar aba ce da ta shafi cigaban tattalin arziki da zamantkewar kasar Sin.

Daidaita matsalar yawan mutane yadda ya kamata ya kasance babbar dawainiya mafi gaggawa ga kasar Sin wajen tabbatar da bunkasar tattalin arziki da samu cigaban zamantakewar al'umma da kuma dauwamamen cigaba.Tun daga shekaru saba'in na karni na 20 gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da manufar kayyade yawan haihuwa a duk fadin kasar Sin ba tare da kasala ba.Ta tsaya a kan wayar da kan matasa da suka isa aure su yi jinkirin aure da hayayyafa,haka kuma ta ce namiji daya da mace daya da da ko 'ya daya,bisa ka'idoji da aka tsara wasu iyalai suna iya samun 'ya'ya biyu.Bayan da ta yi gwagwarmaya cikin shekaru talatin da suka gabata,bisa rashin cigaba da take ciki wajen tattalin arziki,kasar Sin ta hana saurin cigaban karuwar mutanenta,hayayyafa ta ragu har ta kai yadda ake bukata,mace macen mutane sun yi ta raguwa,tare da nasara ta samo wata hanyar warware matsalarta wajen yawan mutane,wannan ya taimaka wa kasar Sin wajen bunkasa tattalin arziki da cigaban zamantkewar al'umma da kuma kyautatuwar zaman jama'a,haka kuma ta ba da taimako mai amfani ga batun yawan mutane na duniya baki daya.

1 2