Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-13 17:55:29    
Ana soma kara himma ga yin aikace-aikacen al'adu domin wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan Adam

cri

Wani mashahurin mai yin zane-zane na kasar Sin mai suna Huang Yongyu ya yi wani zanen da ke da babban batu a kan Jamhuriyar kasar Kenya , wato tsuntsayen flasmingos a cikin tabkin Nakuru, ta hakan, ya bayyana halayen musamman da ake ciki a nahiyar Afrika. A gun bikin budewar nunin, Mr Huang Yongyu ya bayanna cewa,bisa matsayina na wani tsoho mai yin zane-zane da ke da shekaru 84 da haihuwa, na shiga cikin aikace-aikacen nuna fasahohi da ke da ma'anar kagowa a tarihi a lokacin da nake duniya, na yi farin ciki sosai. A lokacin da ake maraba da zuwan ranar yin wasannin Olimpic , an bayyana sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yin zane-zane, wannan ne alfaharin ga masu yin zane-zane na kasar Sin, hakan kuma alfahari ne ga rukunin masu yin zane-zane na kasar Sin.

Mun sami labari cewa, za a shirya nunin a sauran wuraren kasar Sin tare da babbar hedkwatar Majalisar Dinkin duniya da sauran hedkwatocin kasashe fiye da goma na duniya.

A watan Mayu kuma, gidan baje kolin kayayyakin tarihi na birnin Beijing da sauran gidajen yin nune-nunen fasahohi su ma sun shirya nune-nunen al'adu har sau fiye da 100. Mataimakin shugaban hukumar kare kayayyakin tarihi na birnin Beijing Mr Shu Xiaofeng ya bayyana cewa, bisa shirin da aka tsara, an ce, za a shirya nune-nune na gida da na waje har da yawansu ya kai 400. Ya ce, daga ranar nan zuwa ranar da ake soma wasannin Olimpic na shekarar 2008, za a shirya nune-nunen da yawansu ya kai 200 cikin dogon lokaci, sa'anan kuma za a shirya nune-nunen da yawansu zai kai 200 cikin dan gajeren lokaci.

Yanzu, an rage shekara daya da wasu watanni don shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008, birnin Beijing zai shirya aikace-aikacen al'adu da yawa domin maraba da zuwan ranar yin wasanin Olimpic na shekarar 2008.(Halima)


1 2