Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-13 17:55:29    
Ana soma kara himma ga yin aikace-aikacen al'adu domin wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan Adam

cri

Za a yi wasannin Olimpic na 29 a shekarar 2008 a birnin Beijing. Don mai da muhimmanci ga tunanin shirya wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'Yan Adam, daga watan Mayu na shekarar da muke ciki, bi da bi ne ake shirya aikace-aikacen al'adu domin wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan adam, duk domin kara himma ga shirya wasannin Olimpic na Beijing.

A farkon watan Mayu, bisa matsayin daya daga cikin manyan aikace-aikacen al'adu da ake yi domin wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan adam, an yi nunin farko a birnin Beijing na kasar Sin dangane da fasahar zane-zanen da masu yin zane-zane na kasar Sin suka yi kan babban iyalin Majalisar Dinkin duniya , wato kasancewa cikin duniya daya. A gun bikin budewar nunin, wani jami'in ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin wanda shi ne daya daga cikin wadanda suka shirya nunin Mr Li Bing ya bayyana cewa, wannan ne aikin da ba a taba yi ba, mun gayyaci nagartattun masu yin zane-zane 200 na kasar Sin ciki har da na Hongkong da na Taiwan don yin zane-zane na sifantar da almomin kasashe 192 da ke cikin Majalisar Dinkin Duniya da na hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Wadannan masu yin zane-zane na kasar Sin sun yi zane-zanen da ke kunshe da samfurorin tsohon tasmaharan Lahaur na kasar Bakistan da gidan nuna wasannin kwaikwayo tare da wake-wake da kide-kide na Sydney na kasar Australiya da mutum mutumi na "Little Mermaid" na kasar Denmark da shagalin Rose na kasar Bulgaria da wasan raye-raye irin na Tango na kasar Argentina da dai sauransu tare da kayayyakin al'adu na tarihi da gine-ginen tarihi da al'adar gargajiya da furannin mukin kasa da tsuntsayen mulkin kasa da dai sauransu wadanda suka iya wakiltar halayen musamman na wadannan kasashe ta hanyar yin amfani da fasahar yin zane-zanen kasar Sin. Suna da kyaun gani sosai da sosai.

1 2