Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-12 19:07:43    
Kasar Sin ta dauki matakan fama da bala'in ambaliyar ruwa a yankunan kudancinta

cri

Jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ma tana fama da bala'in ambaliyar ruwa sosai. Bisa kididdigar da ofishin ba da umurnin fama da bala'un ambaliyar ruwa da fari na jihar ya bayar, an ce, yawan mutanen jihar da ke fama da bala'in ambaliyar ruwa ya kai fiye da miliyan 2 da dubu dari 1, mutane fiye da 10 sun mutu a cikin bala'in. Yawan hasarar tattalin arziki ya kai kudin Renminbi yuan fiye da miliyan dari 5. Yanzu gwamnatin jihar Guangxi tana fama da bala'in da ba da kayayyakin jin kai yadda ya kamata bisa shirin da ta tsara. Mr. Ye Weiqing, direktan ofishin ba da umurnin fama da bala'u daga indallahi na jihar Guangxi ya ce, "Bayan aukuwar bala'in, gwamnatin jihar ta riga ta ba da umurni ga hukumominta, inda ta neme su da su yi namijin kokari wajen fama da bala'in da ba da agaji domin tabbatar da cewa, jama'ar da ke fama da bala'in sun samu abinci da tufafi da wurin kwana da magunguna."

Mr. Ye ya ce, bayan aukuwar bala'in, shugabanni da ma'aikata na hukumar kula da harkokin jama'a ta jihar da sauran hukumomin gwamnatin da abin ya shafa sun isa wuraren da ke fama da bala'in ba tare da bata kowane lokaci ba domin shirya da ba da umurni da daidaita ayyukan fama da bala'in da samar wa jama'a masu fama da bala'in wuraren kwana na wucin gadi. Yanzu, jama'ar da ke fama da bala'in a shiyyoyi 4 ciki har da birnin Guilin inda aka fi shan bala'in sun riga sun samu abinci da tufafi da matsuguni. Duk wadanda suka kamu da ciwo, ana musu jiyya. Yankunan da ke fama da bala'in suna cikin kwanciyar hankali.

Ban da lardin Guangdong da jihar Guangxi wadanda suka fi shan bala'in ambaliyar ruwa, ana kuma matukar kokarin fama da bala'in ambaliyar ruwa yadda ya kamata bisa shirin da aka tsara a lardunan Hunan da Guizhou a karkashin taimakawar kwararru na ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin. (Sanusi Chen)


1 2