Tun watan Yuni da muke ciki, an sami aukuwar bala'in ambaliyar ruwa mai tsanani a larduna 4, wato Guangdong da Guangxi da Hunan da Guizhou na kasar Sin sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya. Wannan bala'i ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da saba'in tare da mutane fiye da miliyan 10 da suke shan wahalhalu. Yanzu ma'aikata mai kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta riga ta soma aiwatar da shirin fama da bala'u daga indallahi. Gwamnatocin wuraren da suke shan bala'i suna kuma aiwatar da matakan fama da bala'in da samar wa jama'a taimakon da suke bukata. Mr. Liao Yongfeng, wani jami'in da ke kula da aikin fama da bala'u daga indallahi a ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya gaya wa kafofin watsa labaru cewa, "Bayan aukuwar wannan bala'i, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar ta aiwatar da shirye-shiryen fama da bala'in ambaliyar ruwa daban-daban bisa hali daban-daban da ake ciki a lardunan Hunan da Guangxi da Guizhou. Ta kuma aika da rukunonin aiki zuwa yankunan da ke fama da bala'in domin binciken bala'in da nuna jaje ga jama'ar da suke shan bala'in. Sannan kuma sun bai wa gwamnatocin wurin taimako wajen fama da bala'in da ba da agaji."
Mr. Liao ya kara da cewa, yanzu ma'aikatar kula da harkokin jama'a tana yin tattaunawa da sauran hukumomin da abin ya shafa wajen tabbatar da samar da kayayyakin jin kai da kudade ga wuraren da ke fama da bala'in.
Lardin Guangdong ya fi sauran wurare tsanani wajen fama da bala'in. Mr. Zhu Zilong, wakilinmu da ke birnin Guangzhou, hedkwatar lardin ya bayyana cewa, "Ofishin ba da umurnin fama da bala'un ambaliyar ruwa da fari na lardin Guangdong ya riga ya aika da kananan kwale-kwale masu sauri guda 18 tare da ma'aikata fiye da dari 1 zuwa shiyyar Meizhou inda ake shan bala'in ambaliyar ruwa sosai a ran 9 ga wata domin ceton jama'ar da ke shan bala'in dare da rana. Bugu da kari kuma, ya kebe kudaden da suka kai kudin Renminbi yuan miliyan 6 da dubu dari 5 domin aikin gaggawa ga shiyyoyin da ke fama da bala'in."
1 2
|