Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-12 18:04:29    
Babban tsaunin Huangshan mai ban mamaki

cri

Ban da itatuwan pine masu ban mamaki a babban tsaunin Huangshan, saboda akwai kwazazzabai da tuddai da yawa a nan, shi ya sa a kan ko wane babban dutse an sami duwatsu masu ban mamaki da yawa, yawancinsu sun bullo ne yau da shekaru fiye da miliyan 1 da suka wuce. Duwatsun su kan ba mutane mamaki domin sun nuna siffofi daban daban daga wurare daban daban.

Yin yawo a tsakanin babban tsaunin Huangshan, masu yawon shakatawa daga wurare daban daban na duniya sun numfashi danyen iska, sun ji sakin jiki sosai. Malam Wang Lichang ya bayyana cewa, 'A lokacin kuruciyata, ina alla-alla wajen zuwa babban tsaunin Huangshan, amma babu dama. Yau na sami dama in kawo ziyara a nan, a ganina, babban dutsen Huangshan kayan tarihi ne mafi kyau ta fuskar al'adu na al'ummar kasar Sin, ba za a sake samunsa ba, na ji alfahari sosai. Bambancin da ke tsakanin babban tsaunin Huangshan da sauran wurare shi ne akwai kwazazzabai da yawa a nan, kuma itatuwan pine suna girma a tsakanin duwatsu.'

Sa'an nan kuma, madam Yuki Suenaga, wata 'yar kasar Japan, ta gaya wa wakilinmu cewa, 'Babban tsaunin Huangshan wuri ne mai matukar kyau gani, ya fi jawo hankulan Japanawa kwarai, mu Japanawa muna kishin irin wadannan ni'imtattun wurare da gaske, wadanda suka yi kama da zanen gargajiya irin na kasar Sin. Yau na kawo wa babban dutsen Huangshan ziyara, na ji farin ciki sosai saboda ganin wadannan duwatsu da itatuwan pine.'

In muna cewa, itacen pine da duwatsu masu ban mamaki sun yi shekara da shekaru ba su canza ba a babban tsaunin Huangshan, to, ma iya cewa, kallon tekun gajimare a nan na bukatar sa'a. Ya fi kyau a je babban tsaunin Huangshan don kallon tekun gajimare a tsakanin watan Nuwamba na ko wace shekara zuwa watan Mayu na shekara mai zuwa. Malam John Pasden, dan kasar Birtaniya, bai taki sa'a a wannan karo ba, ya ji bakin ciki kadan saboda bai ga tekun gajimare ba. Duk da haka, ya ce, 'Kyawawan wurare masu ni'ima da danyen iska su ne suka jawo hankalina, na kawo wa babban tsaunin Huangshan ziyara, ban da wannan kuma, babban tsaunin Huangshan na daya daga cikin wuraren yawon shakatawa mafi kyau na kasar Sin. Ina tsammani cewa, zan sake zuwa nan don kallon tekun gajimare a lokacin kaka ko kuma lokacin huturu.'


1 2