Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-12 18:04:29    
Babban tsaunin Huangshan mai ban mamaki

cri

A kudancin lardin Anhui da ke tsakiyar kasar Sin, akwai wani babban tsauni da ya yi suna saboda itacen pine da duwatsu masu ban mamaki da kuma tekun gajimare, sunansa babban tsaunin Huangshan, wanda shi ne daya daga cikin shahararrun wuraren yawon shakatawa na kasar Sin, kuma kayan tarihi ne na al'adu da na halitta na duniya.

In an kwatanta shi da sauran manyan duwastu masu ban mamaki da yawa a kasar Sin, sigar musamman mafi girma ta babban tsaunin Huangshan ita ce itatuwan pine masu ban mamaki da ke zama a nan. A cikin babban tsaunin mai tsawon kilomita daruruwa, itatuwan pine suna girma sosai a tsakanin manyan duwatsu. Abu mafi ban mamaki shi ne dukan ganyayemasu siffar kaya na itatuwan pine suna girma a tsaye a babban tsaunin Huangshan, mutane su kan ji samun sabon karfi saboda ganin wadannan itatuwa. Malam Wang Henglai, wani jami'in kwamitin shiyyar yawon shakatawa ta babban tsaunin Huangshan ya yi karin bayani cewa, 'A babban tsaunin Huangshan, itatuwan pine suna girma a wurare masu tsayin misalin mita 800 daga leburin teku, kawunansu sun yi lebur, ganyayansu masu siffar kaya una girma a tsaye, ta haka sun iya samun ruwa da abubuwa masu gini jiki da ke cikin iska, itatuwan pine sun kara girma a cikin mawuyancin hali, saiwoyinsu sun samar da wani irin sinadari da ake kira organic acid a Turance, wanda ya narke duwatsun da ke cikin babban tsaunin Huangshan zuwa taki irin na musamman, itatuwan sun karbe su ta hanyar saiwoyinsu don samun girma. Itatuwan pine suna dacewa da irin wannan muhalli. '

Wurin da ya fi dacewa da kallon itatuwan pine shi ne rumfa mai suna Yupinglou, wadda mashahurin mai yawon shakatawa Xu Xiake na zamanin da na kasar Sin yakira ta da sunan wuri mafi kyau a babban tsaunin Huangshan. A kan kwazazzabon da ke gaban rumfar, an sami shahararrun itatuwan pine 3, sunayensu su ne 'Yingke' da 'Peike' da 'Songke', wato 'maraba da baki' da 'rakiyar baki' da kuma 'yin ban kwana ga baki'. Itacen pine mai suna 'Yingke' ya riga ya zama alamar itatuwan pine na babban tsaunin Huangshan, har ma duk babban tsaunin Huangshan.

A matsayin wani irin itace na musamman na babban tsaunin Huangshan, an riga an tanadi itatuwan pine 54 masu dogon tarihi a cikin takardar sunayen kayayyakin halitta ta duniya tare da babban tsaunin Huangshan. Kiyaye wadannan itatuwa masu daraja na daya daga cikin ayyuka mafi muhimmanci ga shiyyar yawon shakatawa ta babban tsaunin Huangshan.

1 2