Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-29 19:11:27    
Manyan tabkuna 5 da suke hade da juna a lardin Heilongjiang na kasar Sin

cri

Ko da yake manyan tabkuna 5 da ke hade da juna suna da asali iri daya, amma suna da sigar musamman tasu. Duk da haka, kifayen da aka kama daga tabkunan 5 suna da dandano sosai, kuma mutanen wurin sun fi son cinsu. Malam Zhao Ming, wani mazaunin wurin, ya bayyana cewa, 'A wani lokaci, kifayen da aka kama daga sauran tafkuna ba su da dadin ci, amma wadanda aka kama daga wadannan manyan tabkuna 5 sun girma a cikin dogon lokaci, namunsu na da dadin ci, sa'an nan kuma, bayan da muka kama su daga tabkin, mun dafa su a cikin ruwan tabkunan mai ma'adinai, ma iya cewa, mun dafa kifi a cikin ruwan tabkin da yake zama.'

Ko da yake irin wannan kifi na da matukar dadin ci, amma an tsara tsattsauran matakai don kiyaye muhalli a shiyyar shakatawa ta manyan tabkuna 5 da ke hade da juna, shi ya sa ba safai a kan ci irin wannan kifi a ko wane lokaci ba. Madam Zhang Lijun, shugaban hukumar yawon shakatawa ta shiyyar shakatawa ta manyan tabkuna 5 ta yi karin bayani cewa, 'Hukumarmu tana raya shiyyar kiyaye halitta da kuma wurin shakatawa na manyan tabkuna 5 da ke hade da juna bisa shirye-shiryen da aka tsara. Ga misali, a cikin lokacin hana kama kifi, kada a kama kifaye daga wadannan manyan tabkuna 5.'

A kewayen manyan tabkuna 5 masu cike da ruwa mai tsabta, akwai manyan duwatsu masu aman wuta guda 14. Tsayinsu na tsakanin mita 400 zuwa mita 600 daga leburin teku. Suna da girma sosai, su ne daya daga cikin bakaken manyan duwatsu masu aman wuta da aka fi adana su yadda ya kamata a duk duniya, kuma masu yawon shakatawa da yawa sun fi son ziyarar wadannan manyan duwatsu masu aman wuta a kan hanyarsu ta ziyarar kyawawan manyan tabkuna 5 da ke hade da juna.

Saboda barkewar manyan duwatsu masu aman wuta, an samu ruwa mai ma'adinai mai dimbin yawa a wannan shiyyar manyan tabkuna 5 da ke hade da juna. Ruwan mai ma'adinai ya yi kama da lemu, amma yana da dan yaji kadan. Mutane sun iya shan shi, kuma sun iya wanka da shi, abubuwa masu gina jiki ire-ire 10 ko fiye da ke cikin ruwan na iya shawo kan ciwon ciki da na fata da hawan jini da tabuwar kwakwalwa da dai sauransu.

A ko wace shekara mutane masu yawa sun kai ziyara a manyan tabkuna 5 da ke hade da juna saboda sunansu, ba kawai sun yi yawon shakatawa a nan ba, har ma sun yi zama a cikin cibiyoyin hutawa a cikin dogon lokaci, inda suka shawo kan cututtukan da suke fama ta hanyar yin amfani da ruwa mai ma'adinai da kuma tabon da aka samu a manyan duwatsu masu aman wuta. Ban da wannan kuma, don bai wa masu yawon shakatawa sauki, an samar da kananan rumfuna a ko wane bakin idon ruwa a manyan tabkuna 5, bayan haka kuma, a kewayensu, an fito da famfo da yawa, da zarar masu yawon shakatawa sun bude famfon, sai sun iya shan danyun ruwa mai ma'adinai.


1 2