
Masu sauraro, a lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, akwai wurin yawon shakatawa na manyan tabkuna 5 da suke hade da juna, inda aka fi samun cikakken tsarin kasa irin na dutse mai aman wuta a nan, kuma an fi adana shi yadda ya kamata, in an kwatanta shi da sauran wurare a duk duniya, shi ya sa masu ilmin kimiyya suke kira wannan wuri 'dakin nune-nunen duwatsu masu aman wuta na ikon Allah', sa'an nan kuma, gwamnatin Sin ta mayar da wadannan manyan tabkuna 5 da ke hade da juna da su zama daya daga cikin wuraren shakatawa na kiyaye yanayin kasa na duniya na rukuni na 1.

Shiyyar da manyan tabkuna 5 da ke hade da juna suke ciki wuri ne da aka fi samun barkewar duwatsu masu aman wuta. Barkewar duwatsu masu aman wuta da aka samu a shekara ta 1719 ta zama sanadiyyar bullowar wadannan kyawawan manyan tabkuna 5, wato bayan da duwatsu masu aman wuta suka barke yau da shekaru fiye da 200 da suka wuce, tabo mai kauri ya daskare sannu a hankali, ya zama bakaken duwatsu, duwatsun kuma sun toshe wani kogi mai suna Baihe, wanda ke gangara a wannan shiyya, ta haka an sami manyan tabkuna 5 masu kyan gani, wadanda suke hade da juna, su ne wadanda mutane ke gani a yau. Mutanen wurin sun kira wadannan tabkuna 5 da ke hade da juna da sunan tabki na 1 da na 2 da na 3 da na 4 da na 5. Mataimakiyar shugaba Zhang Lili ta wurin shakatawa na manyan tabkuna 5 da ke hade da juna ta yi karin bayani cewa, 'Wadannan tabkuna 5 suna hade da juna, ruwa ya fito daga karkashin kasa a tabki na 5. Tabki na 3 ya fi girma, fadin ruwa ya kai misalin murabba'in kilomita 21.5. Mutane na iya yin yawo daga tabki na 1 zuwa na 2 cikin kwale-kwale ba tare da gamuwa da shinge ba.'
1 2
|