Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 17:18:28    
An gudanar da harkar daukar labaru a kasar Sin a hukumance a karkashin tutar rangadin sada zumunta tsakanin Sin da Rasha

cri

A nasa bangaren, jakadan kasar Rasha dake nan kasar Sin Mr. Sergei Razov shi ma ya yi jawabi a gun bikin, inda ya furta, cewa: "Na hakkake, cewa harkar daukar labaru da 'yan jarida na Rasha za su yi a kasar Sin za ta samar wa jama'ar Rasha damar samun karin ilmi a game da al'adun gargajiya na kasar Sin wadda take samun bunkasuwa ta hanyoyi da dama, da kuma ganin yadda jama'ar kasar Sin suke more zaman jin dadi".

Ko kuna tune da, cewa a shekarar da ta gabata, gidan rediyon kasar Sin wato CRI da kamfanin dillancin labaru na Tass na Rasha sun yi hadin gwiwa wajen gudanar da wata harkar daukar labarai a Rasha a tutar rangadin sada zumunta tsakanin Sin da Rasha. Game da rangadin da ake yi a kasar Sin, shugaban CRI Mr. Wang Gengnian ya fadi, cewa: " Mutane na kyautata zaton, cewa harkar daukar labaru da 'yan jarida na kasashen Sin da Rasha suke gudanarwa za ta kasance tamkar wani misalin koyo daban na kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen biyu".

'Yan jaridu na kasashen Sin da na Rasha za su dauki wata daya ko fiye wajen yin rangadin gani da ido na tsawon kilo-mita 8,600 a cikin yankin kasar Sin domin bayar da labaru kan yanayin zamantakewar al'umma, da tattalin arziki, da al'adu da kuma na halayen musamman na wuraren kasar Sin.

'Yan jaridun za su dawo nan Beijing ne a karshen wata mai kamawa. An tabbatar da cewa, a lokacin, za a gudanar da wani gagarumin bikin lale marhabin da dawowarsu.( Sani Wang )


1 2