Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 17:18:28    
An gudanar da harkar daukar labaru a kasar Sin a hukumance a karkashin tutar rangadin sada zumunta tsakanin Sin da Rasha

cri

"Yanzu bari in sanar da ku, cewa ayarin gwanon motoci dauke da 'yan jarida na Sin da na Rasha ya tashi"! Nan take, wata babbar kungiyar daukar labaru dake hade da manyan kafofin watsa labaru 16 ciki har da gidan rediyon kasar Sin wa CRI da kuma kamfanin dillancin labaru na Tass na Rasha ta tashi daga filin Tian Anmen na Beijing domin yin rangadin sada zumunta na tsawon kwanaki sama da 30 a kasar Sin.

Wadannan 'yan jaridu za su dauki labarai a larduna da birane da kuma jihohi masu cin gashin kansu 15 na kasar Sin a kyawawan wuraren yawon shakatawa kuma a game da al'adun gargajiya na kabilu daban-daban da kuma yadda ake bunkasa tattalin arzikin kasar Sin; Bugu da kari, za su bayar da jerin labarai kan yanayin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, da zumuncin al'ada dake tsakanin kasashen Sin da Rasha da kuma yanayin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen biyu.

Mr. Wang Taihua, shugaban babbar hukumar kula da harkokin watsa labaru da sinema da kuma na telebijin ta kasar Sin, da Mr.Sergei Razov, jakadan kasar Rasha dake nan kasar Sin da kuma sauran mutane sama da 200 daga sassa daban-daban na kasashen biyu sun halarci gagarumin bikin tashin kungiyar daukar labaru, inda Mr. Wang Taihua ya yi jawabin, cewa: "Ina fatan aminai 'yan jarida daga Rasha za su kai rangadin ganewa ido ga kasar Sin don bayar da labarai na gaskiya kuma masu ban sha'awa, ta yadda sauran aminai masu tarin yawa na Rasha za su kara samun ilmi game da tarihin kasar Sin da kuma fuskarta a yau. Lallai rangadin daukar ziyarar zai kasance tamkar wata gada ce ta zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen Sin da Rasha, wanda kuma zai taka muhimmiyar rawa kan bunkasa kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa ta muhimman tsare-tsare dake tsakaninsu.


1 2