Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:37:06    
Madam Wu Yi ta kira kasashen Sin da Amurka su warware kiki-kakar ciniki da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari

cri

Game da matsalar ciniki maras daidaituwa da kasar Amurka ke mai da hankalinta a kai, Madam Wu Yi ta bayyana cewa, babban dalili shi ne kasashen biyu suna kan matsayin bunkasuwar tattalin arziki ba iri daya ba. Game da haka, ta ce, ya kamata kasashen biyu su nemi dabara domin warware matsaloli a gida. Daga baya, sai daukan matakai masu inganci ta hanyar yin hadin gwiwa, kuma kada wata kasa ta zargi sauran kasashe saboda matsalar kanta ko sa sauran kasashe da su karbi ra'ayinta ta hanyar matsa kaimi da nuna kiyyaya. A zamanin dinkuwar duniya na yau, nuna kiyyaya ba zai warware matsala ko kadan ba.

A karshe dai, Madam Wu Yi ta sake jaddada cewa, kasar Sin tana fatan za ta iya yin kokari tare da kasar Amurka domin warware matsalar cinikin rashin daidaituwa.

Mr. Paulson ya yi jawabi a gun bikin bude shawarwari. Ya ce, "Ba a taba ganin ministocin kasar Sin mai yawan haka suna kasar Amurka a tarihi ba. ? dukanmu mun gane cewa, daidaita huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin yana da muhimmanci sosai!"

Mr. Henry Kissinger tsohon babban sakataren harkokin waje na kasar Amurka kuma ya yi jawabi a gun bikin budwa a matsayin bako na musamman. Ya ce, kasashen Amurka da Sin suna taka muhimmiyar rawa kan harkokin kasashen duniya. Zaman lafiyar kasashen duniya yana bukatar kasashen biyu su kara hadin gwiwa. Ya ce, wannan shawarwari yana da ma'anar tarihi.

Kwanaki biyu ne za a yi shawarwarin na karo na biyu kan tattalin arziki a tsakanin kasashen Sin da Amurka. bangarorin biyu za su yi shawarwari kan fannonin aikin hidima, da zuba jari, da makamashi da muhali, da bunkasuwa mai daidaituwa da aikin kirkire-kirkire.


1 2