Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:37:06    
Madam Wu Yi ta kira kasashen Sin da Amurka su warware kiki-kakar ciniki da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari

cri

A ran 22 ga wata a Washington babban birnin kasar Amurka, an bude shawarwarin na karo na biyu kan tattalin arziki a tsakanin kasashen Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare wanda za a shafiekwanaki biyu ana yi. Madam Wu Yi mataimakiyar firaministan kasar Sin da Mr. Paulson ministan sha'anin kudi na kasar Amurka sun wakilci shugabannin kasashensu biyu sun shugabanci wannan shawarwari tare. Yanzu sai mu saurari labarin da wakilinmu Xu Qinduo da ke kasar Amurka ya jiwo mana mai lakabi haka: Madam Wu Yi ta kira kasashen Sin da Amurka su warware kiki-kakar ciniki da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa.

A gun bikin bude taron, Madam Wu Yi ta tuna da tarihin cinikin da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, inda ta ce, dalilin da ya sa kasashen biyu suka bude wannan shawarwari shi ne, huldar tattalin arziki da cinikin da ke tsakaninsu ta yi ta bunkasuwa da sauri sosai. ta ce, "A lokacin da kasashen biyu suka kafa huldar diplomasiyya, ma iya cewa kasashen babu ciniki tsakaninsu tsakaninsu. Amma, a shekarar 2006, yawan kudin cinikin a tsakaninsu ya kai dolar Amurka biliyan 262.6, kuma yanzu su zama abokan ciniki mafi girma na biyu na juna. A sa'I daya kuma, musanyar da ke tsakaninsu kan fannonin siyasa, da aikin soja, da al'adu, da kimmiya da fasaha, da kuma yawon shakatawa ta yi ta karuwa."

Madam Wu Yi ta ce, aminci  tsakanin juna da kuma huldar hadin gwiwa sun dace da babbar moriyar kasashen biyu. Ta ce, kasashen biyu ba kasashen da moriya ta shafa ne kawai ba, kuma su ne kasashen da ke yin hadin gwiwa,kuma yin shawarwari cikin adalci, yin hadin gwiwa domin moriyar juna sun zama jigun mu'amala na kasashen biyu.

Ta ce, akwai kasancewar sabannin ra'ayin da ke tsakanin kasashen biyu, ya kamata a warware matsaloli ta hanyar shawarwari, kuma a kau da matsalolin tattalin arziki da ciniki wanda zai shafi harkokin siyasa. Ta ce, "Yanzu huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen biyu ta shafi fannoni daban daban, ya kamata mu kara moriyar juna ta hanyar yin aiki mai inganci. Kuma mu kwantar da hankulanmu domin warware matsaloli da rikici yadda ya kamata. Kuma kada a mayar da batun tattalin arziki da ya zama batun siyasa, wannan ba zai warware matsala ba, kuma zai kawo mugun tasiri sosai ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu."


1 2