Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:37:00    
Shanghai tana share fagen taron wasannin Olympic na musamman na duniya yadda ya kamata

cri

Sakamakon bincike da aka samu ya nuna cewa, akwai nakasassu misalin miliyan 83 a kasar Sin, ciki har da masu tabin hankali fiye da miliyan 9, wadanda suka hada da 'yan wasan Olympic na musamman dubu dari 5 ko fiye. Shugaban hadaddiyar kungiyar harkokin nakasassu ta kasar Sin madam Tang Xiaoquan ta bayyana cewa, wasannin Olympic na musamman zai taka rawa mai yakini kan masu tabin hankali da sha'anin nakasassu da kuma bunkasuwar zaman al'ummar kasa. Ta ce,

'Masu tabin hankali suna iya motsa jiki da kyautata karfinsu da ingancin jikunansu ta hanyar shiga wasannin Olympic na muasmman. A lokacin da suke shiga wasannin Olympic na musamman, suna bukatar tuntubar mutane da yawa, sun shiga zaman al'ummar kasa, suna tuntubar halitta, ta haka za a kyautata kwarewarsu a fannonin fahimta da yin cudanya da sauran da kuma yin magana, kazalika kuma za a bunkasa tunaninsu. Za su sami babban ci gaba wajen samun sauki da kuma kyautata kwarewar shiga cikin harkokin zaman al'ummar kasa cikin adalci a nan gaba. '

Wannan jami'a ta kara da cewa, shirya taron wasannin Olympic na musamman na sanya masu koshin lafiya da kuma masu tabin hankali su kara yin cudaya da juna, don haka, za a fito da kyakkyawan yanayi a zaman al'ummar kasar Sin, wato ana taimakawa da goyon baya da kuma kula da masu tabin hankali a kasar Sin.(Tasallah)


1 2 3