Za a yi taron wasannin Olympic na musamman na duniya na shekara ta 2007 a birnin Shanghai na kasar Sin a watan Oktoba na wannan shekara, shi ne karo na farko da za a yi taron wasannin Olympic na musamman na duniya a wata kasa mai tasowa, a lokacin taron, 'yan wasa da malaman horaswa fiye da dubu 10 da iyayen 'yan wasan da kwararru da masana da kuma baki fiye da dubu 20 daga kasashe da yankuna sama da 160 za su halarci wannan gaggarumin taro. Yanzu ana share fagen wannan taron wasannin Olympic na musamman na duniya daga dukkan fannoni yadda ya kamata.
Taron wasannin Olympic na musamman taron wasannin motsa jiki ne na musamman da kwamitin wasannin Olympic na musamman na duniya ya shirya domin masu tabin hankali na duk duniya. 'Yan wasa suna yin takara da juna a cikin kungiya-kungiya bisa shekarunsu da kwarewarsu, ba a samar da matsayin bajimta na duniya ba, kuma dukkan 'yan wasan da suka shiga gasanni za su sami lambobin yabo.
1 2 3
|