Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 10:51:29    
Ya kamata, a mayar da inganta hadin kan masana'antu bisa matsayin babbar manufar hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arziki

cri

Bayan haka Mr Wu Bangguo ya kara da cewa, hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika a fannnin tattalin arziki da cinikayya yana da makoma mai kyau. Ya jaddada cewa, ya kamata, a mayar da inganta hadin kan masana'antu bisa matsayin babbar manufa game da hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya. Ya ce, "masana'antu su ne ginshikin kasuwanni da na zuba jari da kuma hadin kan tattalin arziki da cinikayya. Babu yadda za a yi a inganta hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afrika, sai masana'antu su nuna himma wajen shiga hadin kan. Yana fatan masana'antun Sin da Afrika za su inganta hadin kansu bisa halin da ake ciki, kuma bisa ka'idojin zaman daidaici da moriyar juna, da yin hadin kai don samun nasara tare, su tabbatar da sakamako da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika, su rubuta sabon shafin hadin guiwar Sin da Afrika tare."

Mr Mohamed El Masry, shugaban kungiyar tarayyar masana'antu da kasuwanci ta Afrika ya yi jawabi a gun taron, inda sosai da sosai ya darajanta muhimmancin taron koli na dandalin tattauna kan hadin guiwar Sin da Afrika. Ya ce, "yau muna zaman taro a nan ne domin yin kokari sosai wajen gaggauta bunkasa huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare, kuma za mu sa kaimi ga bunkasa harkokin cinikayya a tsakaninsu. Yayin da muke aiwatar da shawarwari da kasar Sin ta gabatar dangane da gaggauta bunkasa tattalin arzikin Afrika, na hakake, ko shakka babu, za mu sami ci gaba da wadata da arziki ta hanyar hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afrika a fannoni daban daban. Ina son in yi amfani da wannan dama, in bayyana muhimmancin hadin kan kudu maso kudanci. Sin da Afrika za su kara kokari tare wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da wadata ga mutanensu da suka dauki sulu'in duk mutanen duniya, su fuskanci kalubale da ake yi musu tare, yayin da ake bunkasa tattalin arzikin duniya da na yankuna. "(Halilu)


1 2