Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 10:51:29    
Ya kamata, a mayar da inganta hadin kan masana'antu bisa matsayin babbar manufar hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arziki

cri
A ran 21 ga wata, Mr Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki ta aminci a kasar Masar ya halarci babban taro kan hadin guiwar masana'antu na Sin da Afrika da aka shirya a birnin Alkahira. Inda ya bayar da jawabi mai lakabi haka, "a yi kokari tare don rubuta wani sabon shafi ga hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika. A cikin jawabinsa, ya nuna cewa, ya kamata, a mayar da inganta hadin kan masana'antu bisa babbar manufa game da hadin guiwar Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da cinikayya.

A watan Nuwamba na shekarar bara, shugabannin kasashen Afrika 48 sun halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika. A gun taron, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bayyana manufofi da matakai da gwamnatin kasar Sin za ta dauka nan da shekaru uku masu zuwa, don inganta hadin guiwarta da Afrika bisa halin da ake ciki. A gun taron da aka yi a wannan rana a birnin Alkahira, Mr Wu Bangguo ya yi bayani a kan yadda ake aiwatar da manufofin da matakan da kasar Sin ke dauka don inganta hadin kanta da Afrika. Ya ce, "yanzu, kasar Sin ta riga ta rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin ba da gudummowa a tsakaninta da kasashen Afrika 17, kuma ta riga ta daddale yarjejeniyoyin ba da rancen kudi mai gatanci a tsakaninta da kasashen Afrika 6, haka kuma ta kulla yarjejeniyoyin soke basussuka da kasashen Afrika 14 suka ci daga wajenta, a shekarar nan za a kammala duk ayyukan soke basussuka guda 81 da sauran kasashen Afrika 19 suka ci daga wajenta. Kazalika yawan ire-iren kayayyaki marasa harajin kwastan da kasar Sin ke shigowa daga kasashen Afrika mafi talauci wadanda suka kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu da kasar Sin ya karu daga 190 zuwa 440. "


1 2