Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-11 14:58:46    
An yi bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar gudun yada kanin wani na mikar wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing

cri

An kiyasta, cewa za a dauki kwanaki 130 wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula a kan hanya mai tsawon kilo-mita 130,000. Shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Mr. Liu Qi ya yi jawabi a gun bikin, inda ya furta cewa: " Wannan dai, wata harkar bai wa juna wutar yula ce da za a fi samun yawan mutane wajen gudanar da ita kan hanya mafi tsawo dake wurare mafi fadi a tarihin wasannin Olympic na zamani. Muna fatan harkar yada kanin wani na mika wutar yula ta taron wasannin Olympic na Beijing za ta sake yayata ra'ayin Olympic zuwa duk duniya da kuma bayyana zafin nama sosai da jama'ar kasar Sin suka nuna don ingiza wasannin Olympic; A lokaci daya kuma, za ta iya gwada kyakkyawar fuska da al'adun gargajiya da kuma halayyar jama'a na biranen kasashe daban-daban da wutar yula za ta ratsa, da kara samun fahimtar juna da dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashe daban-daban; dadin dadawa, za ta iya kara yada babban take a kan cewa 'Duniya daya kuma buri daya' na taron wasannin Olympic na Beijing.

Mr. Jacque Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa shi ma ya yi jawabi a gun bikin, cewa: " Na yi farin ciki matuka da ganin, cewa hanyar gudun yada kanin wani na mika wutar yula za ta ratsa ta hanyar siliki dake da ma'anar tarihi wadda kuma ta alamanta wata hanyar cinikayya da ta hada kasar Sin da sauran kasashen duniya a can can zamanin da; ban da wannan kuma za a bai wa juna wutar yula mai tsarki ta Olympic a wasu wuraren da ba a taba yin haka ba a da".


1 2 3