Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-11 14:58:46    
An yi bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar gudun yada kanin wani na mikar wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing

cri

Jiya da dare, a ginin cibiyar sabon karni dake nan birnin Beijing, an yi gagarumin bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar gudunyada kanin wani na bai wa juna wutar yula da za a bi domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, wanda yake janyo hankulan mutanen duk duniya.

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sake da cewa, tun bayan da gudanar da harkar bai wa juna wutar yula a karo na farko a gun taron wasannin Olympic na Berlin a shekarar 1936, harkar mika wutar yula ta rigaya ta taka mihimmiyar rawa wajen yayata al'adun Olympic a matsayin wata harka da mutane mafi yawa ke halarta, ta kuma kasance wani muhimmin kashi na tarurukan wasannin Olympic da aka gudanar a da. A gun bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar da za a bi wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula da aka gudanar jiya da dare, Madam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin da Mr. Hein Verbruggen, shugaban kwamitin sulhunta harkokin taron wasannin Olympic na Beijing a karkashin tutar kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa sun cire kyallen wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing tare; Daga baya, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Luo Gan da shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa sun yi shelar hanyar da za a bi wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula. Za a gudanar da wannan harka ne a fadin duk duniya, wato ke nan tun daga watan Maris na shekara mai zuwa, za a soma gudun yada kanin wani na mika wutar yula daga nan Beijing zuwa birane 22 na ketare da kuma birane da yankuna 113 na cikin yankin kasar Sin. Kuma a ran 8 ga watan Agusta da dare wato a lokacin bude taron wasannin Olympic, za a dawo da wutar yula cikin babban fili na gudanar da bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing.


1 2 3