Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 19:23:23    
Kallon jerin fitilu a Huangyuan na lardin Qinghai

cri

Ran 4 ga watan Maris na wannan shekara bikin nuna fitilu ne bisa kalandar Sin. An bude bikin fasahar jerin fitilu na Huangyuan a karo na farko a birnin Xining na lardin Qinghai. A ran nan da dare, jerin fitilu fiye da dari 4 na Huangyuan sun ba da haske sosai a gaban masu yawon shakatawa na gida da na waje. Mutane suna yawo a tsakaninsu, tamkar suna yawo a cikin kogin taurari.

A gun bikin fasahar jerin fitilu na Huangyuan da aka yi a shekarar da muke ciki, an gwada fasahar kera jerin fitilu ta hanyar gargajiya tare da cusa sabbin danyun kayayyaki na zamani a ciki, saboda haka ne zane-zanen da ke kan fitilu suka kara samun kyan gani a sakamakon yin amfani da wasu tsoffin fasahohin gargajiya na kasar Sin, kamar su tsala dinki da wasan Piying da yanke takarda da dai makamantansu. An yi zane-zane game da adabi da labarun gargajiya da ke barbazuwa a kasar Sin, da kuma shahararrun wuraren shakatawa da wuraren gargajiya da ni'imtattun wurare na Qinghai, wadanda suka nuna abubuwan da ke shafar dan Adam da labarin kasa na kasar Sin. Malam Ren Yugui, wani mai fasahar gargajiya na Qinghai, ya yi bayanin cewa,'An yi zane-zane a kan jerin fitilu dangane da almara da labarun tarihi da labarun gargajiya da dai sauransu. In an yi nazari kan tarihinsa, an iya gano cewa, jerin fitilu na Huangyuan wani abu ne da aka samar da shi ta hanyar hada al'adun gargajiya da kimiyya da fasaha na zamani tare.'

A shekarun baya da suka wuce, hukumar Huangyuan ta raya jerin fitilu na Huangyuan a matsayin alamar al'adu, ta zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan fiye da miliyan daya kan kafa kamfanin musamman mai kula da nazari da bunkasa jerin fitilu, da sayen injuna, da tattara da kuma kyautata labarai, da horar da wadanda za su gaji fasahar jerin fitilu, da buga littattafan yada fasahar, da gayyatar kwararru da masu fasaha a fannin kiyaye da sabunta fasahar jerin fitilu ta gargajiya. Shugabar hukumar Huangyuan madam Ma Yuying ta bayyana cewa, 'Jerin fitilu na Huangyuan kyakkyawan kayan fasaha ne da ke kunshe da al'adu iri daban daban. Muna maraba da bakinmu na kasashen duniya da su zo Qinghai, su zo garinmu Huangyuan don kallon jerin fitilu, za su kara fahimtar kyawawan fasahohin gargajiya na Huangyuan.'


1 2