Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 19:23:23    
Kallon jerin fitilu a Huangyuan na lardin Qinghai

cri

A gundumar Huangyuan ta lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin, wani irin kayan fasaha na gargajiya mai sigar musamman ya yi shekaru fiye da dari 2 yana samun karbuwa sosai a tsakanin al'umma, sunansa jerin fitilu na Huangyuan. Siffofinsu sun sha bamban da juna, launukansu na nan iri daban daban, an kuma yi zane-zane iri daban daban a kansu, shi ya sa suka jawo hankulan mutane sosai. A shekarar 2005 da ta gabata, an tanadi jerin fitilu na Huangyuan a cikin shirin kasar Sin kan kiyaye abubuwan tarihi na al'adu da ba su kai na a-zo-a-gani ba a rukuni na farko.

Malam Jing Shi ya yi shekaru da dama yana nazarin jerin fitilu na Huangyuan. Ya bayyana cewa, jerin fitilu na Huangyuan na da dogon tarihi, an fara kera shi a tsakiyar zamanin daular Qing, wato yau da shekaru fiye da 200 da suka wuce. A lokacin can, 'yan kasuwa da suka zo Huangyuan daga wurare daban daban sun kera allunan talla na kantunansu, wadanda suka kunna kyandir a ciki, don jawo hankulan masu sayayya da dare. Bayan wannan kuma, an kara kyautata wadannan allunan talla na kantuna, sun kara samun kyan gani, har ma sun zama jerin fitilu, wadanda suke da gindi, siffofinsu na shan bamban, an kuma yi zane-zane iri daban daban a kansu, daga baya kuma, an yi musu kwaskwarima, har ma sun iya ketare tituna.

Jerin fitilu sun hada da fitilu da yawa, ko wanensu kayan fasaha ne. An iya rataya jerin fitilu, ko kuma sa su a doron kasa. Da farko an kera sigogin jerin fitilun da katako, siffofinsu suna kama da na furen plum blossom ko mai kaman shan soro ko kuma mafifici irin na kasar Sin, an yi sassakan zane-zanen gargajiya a kan sigogin katako. Daga baya an rufe sigogin da yadudduka marasa kauri, bisa bambam sigogin ne aka yi zane-zane a kan wadannan yadudduka marasa kauri dangane da labarun gargajiya da al'adu da yanayin wurin da tatsuniyoyi da almara da mashahuran labaru, wadanda suka samu karbuwa sosai a tsakanin mutanen wurin. Malam Jing ya kara da cewa, a duk dare, an kunna jerin fitilu da yawa a kan titunan Huangyuan, an gada wannan al'ada tun can da har zuwa yanzu. A ran 15 ga watan Janairu na ko wace shekara bisa kalandar kasar Sin, a kan shirya bikin nuna jerin fitilu a nan. Malam Jing ya ci gaba da cewa, 'Sinawa suna da al'adar shirya bikin fitilu a ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar kasar Sin, shi ya sa mutanen Huangyuan suka fito da jerin fitilu masu sigar musamman bisa tushen wannan al'ada. A daren ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar Sin, daruruwan fitilu sun haska titi sosai.'

1 2