Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-04 18:32:59    
Amadou Toumany Toure ya sake zama shugaban Mali

cri

Na biyu kuma, gwamnatin Toure ta kyautata hulda a tsakaninta da bangarori daban daban, ta sami amincewa da taimako daga wajensu. Gwamnatin Toure ta dora muhimmanci kan hada kanta da sauran kasashen Afirka, ta sa kaimi kan sada zumunta a tsakaninta da kasashen da ke makwabtaka da ita, ta kuma zabura wajen ci gaban dinkuwar Afirka gaba daya. Sa'an nan kuma, ta shiga cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya a yankunan Afirka ta Tsakiya da ta Yamma cikin himma da kwazo, ta mai da hankali kan karfafa tasirinta a yankin da take ciki. Mr. Toure ya jaddada cewa, ya kamata a tafiyar da harkokin diplomasiyya domin taimakawa bunkasuwar tattalin arziki. Ba kawai ya dora muhimmanci kan raya hulda a tsakanin Mali da kasashen yamma ba, har ma ya jaddada yin hadin gwiwa tare da manyan kasashe masu tasowa. Manufofin da yake aiwatarwa a fannin harkokin diplomasiyya, wato kara samun sabbin abokai da rashin samun abokan gaba sun kyautata sunan Mali a yankin da take ciki har ma a duk duniya, sun kuma ba da taimako wajen samun tallafi da yawa, jama'ar Mali ba kawai sun kyautata mutuncinsu da kuma aniyarsu ba, har ma sun ci gajiya daga wajen wadannan tallafi masu dimbin yawa.

Na uku kuwa, manufofin dimokuradiyya da gwamnatin Toure ke aiwatarwa sun karfafa aniyar da masu kada kuri'a ke nuna masa. A watan Maris na shekarar 1991, Mr. Toure ya yi juyin mulki, ya kafa gwamnatin soja na wucin gadi, amma ya mayar da mulkin kasar ga jama'ar Mali da kansa, an yi babban zabe a shekarar 1992, Alpha Oumar Konaré ya zama shugaban kasar, ya kuma ci gaba da aikinsa tun daga watan Mayu na shekarar 1997. A watan Mayu na shekarar 2002, Mr. Toure ya zama shugaban kasar a matsayin dan takara mai zaman kansa. Mayar da mulkin kasa ga jama'a da Mr. Toure ya yi ya sami babban yabo daga kasashen duniya, nasarar da ya yi a cikin babban zaben ta kuma shaida karfinsa da tasirinsa.

Ko da yake kwamitin tsarin mulkin kasar na bukatar tabbatar da sakamakon babban zaben a karshe, amma ko kusa babu tantama Mr. Toure zai ci gaba da aikinsa a matsayin shugaban Mali.(Tasallah)


1 2