Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-04 18:32:59    
Amadou Toumany Toure ya sake zama shugaban Mali

cri

Ran 3 ga wata, ma'aikatar kula da yankin kasa da ayyukan kananan hukumomi ta kasar Mali ta gabatar da sakamakon babban zabe, Amadou Toumany Toure, shugaba mai ci yanzu na Mali ya ci nasara a cikin zaben a zagaye na farko saboda samun kuri'un da yawansu ya kai misalin kashi 68.3 cikin kashi dari.

Muhimman dalilan da suka sa Mr. Toure ya sami babban rinjaye a cikin babban zaben su ne domin da farko, Mr. Toure ya aiwatar da manufofi masu kyau a wa'adin aikinsa a matsayin shugaban kasar, ta haka a shekarun nan da suka wuce, Mali ta sami kwanciyar hankali ta fuskar siyasa, ta kuma sami saurin bunkasuwar tattalin arziki, zaman rayuwar jama'ar Mali na ta samun kyautatuwa. Wannan kasa ta taba shan fama da rashin kwanciyar hankali a sakamakon juyin mulki da aka yi har sau 2 a tarihinta. Bayan da Mr. Toure ya kama mukaminsa na shugaban Mali a shekarar 2002, ya jaddada samun sulhuntawa da hadin kai a tsakanin al'ummomin kasar, ta haka an sami kwanciyar hankali mai dorewa a fannin siyasa a Mali.

Bayan da Mr. Toure ya fara aiki, ya dora muhimmanci kan raya aikin gona da kara zuba kudi kan albarkatun kwadago da kuma yin gyare-gyare kan tsarin gudanar da ayyukan gwamnatin, shi ya sa tattalin arzikin kasar ya yi ta samun kyautatuwa, yawan karuwar tattalin arziki a shekarar bara ya wuce kashi 5 cikin kashi dari. A sa'i daya kuma, ya mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'arsa, ya mai da muhimmanci kan daidaita batutuwa dangane da zaman rayuwar jama'a, kamar su samun aikin yi da aikin ba da ilmi da kyautata aikin lafiya, saboda haka ya sami babban yabo daga fararen hula. A cikin babban zaben da aka yi a wannan karo, Mr. Toure ya yi alkawarin cewa, idan ya ci babban zaben, zai kara gina asibitoci da makarantu da hanyoyi, zai sanya yawan karuwar tattalin arzikin kasar zai kai kashi 7 cikin kashi dari. Nasarorin da ya taba ci da kuma shirin da ya tsara sun taimaki Mr. Toure da ya sami goyon baya sosai.

1 2