A duk lokacin da suke nuna wasanni, masu yin wasa da kayan kida su kan sa tufafi irin na zamanin da sun yi wasa da tsoffin kayayyakin kida ta hanyoyin gargajiya. Hakan ya sanya masu yawon shakatawa ba su san zamanin da suke ciki ba. Madam Li Hong, wata manazarta ta gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan ta bayyana cewa, kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin ta farfado da kayayyakin tarihi na al'adun kide-kide na zamanin da, a wani bangare daban kuma, yin wasa da wadannan tsoffin kayayyakin kida hanya ce daban da ake nuna su.
Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan ya waiwayi kayayyakin kida ire-ire fiye da 20 don sake fitowa da kide-kide masu tarihin dubban shekaru, ya kuma kafa kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin a shekara ta 2000 don nuna kide-kiden gargajiya na kasar Sin, yanzu kungiyar ta riga ta samar da tsoffin kide-kide misalin 200.
Ba masu yawon shakatawa na gida da na waje kawai ba suke sha'awar more idanun da kyawawan kayayyakin gargajiya iri daban daban da kuma sauraren kide-kiden gargajiya masu dadin ji da aka fito da su da kayayyakin kide na zamanin da, har ma shugabannin kasashen Korea ta Kudu da Tanzania da Thailand da dai sauransu su ma sun mai da hankulansu, sun nuna babban yabo. Madam Wu Hong, wadda ta zo daga lardin Taiwan na kasar Sin, ta ce, 'Yau na ga kayayyakin gargajiya da yawa a nan, na saurari kide-kide masu dadin ji da aka fito da su da kayayyakin kide da aka waiwaya, na ji farin ciki sosai.'
A karshen bikin kide-kide, kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin ta kan gayyaci masu yawon shakatawa da su shiga cikin wasanni. Ga shi, bakinmu na kasar Faransa sun rera wata wakar gargajiya ta garinsu tare. An sami jituwa ne a cikin wannan waka, wadda masu yin wasa da kayan kida na kasar Sin da bakinmu na kasashen waje suka samar da ita ta hanyar hada kayayyakin kida na zamanin da da kide-kiden zamani tare. Idan ana cewa, gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan yana nuna tarihin kabilar Sin ga masu yawon shakatawa na gida da na waje, to, ma iya cewa, kide-kiden gargajiya na kabilar Sin da kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin ta fito da su sun nuna wa jama'ar duniya sigogin musamman da kyan gani na kabilar Sin. 1 2
|